Yadda za a yi kwalli ya lokacin damina
Mata da dama ba su cika son yin kwalliya a
lokacin damina ba. Domin suna tsoro ka da a fara ruwan saman da zai wanke musu
wannan kwalliyar, ko kuma ta cabe musu ita. Sau da yawa ana tambaya wai shin
wace irin kwalliya ce ta dace a yi a lokacin damina? Don haka ne a yau na kawo
muku yadda za a magance wadannan matsalolin ta hanyan sauki.
1.==> Akwai wasu irin hodar fandesho masu santsi
kamar mai. Irin su ne ya kamata a yi amfani da su a lokacin damina, domin ko da
ruwan ya taba fuskar, ba za ta wanke fuskar ba. A nemi irin wannan hodar
fandesho din domin samun sauki ga lamarin
2.==> Akwai wata ‘waterproof mascara’ abin nufi a
nan s hi ne ruwa ba ya ratsa cikinta. Irin shi ne ya kamata ‘yan mata da manyan
mata na amfani da su a wannan lokacin. Idan ba a yi la’akari da samin irin
wannan mascara ba to a sani cewa kwalliyar za ta cabe sosai.
3.==> Kada a manta da lema a duk lokacin da za a
fita domin ba za a san lokacin da ruwan zai sauko ba.
4.==> A kasance tare da abin rufe kai. Domin yawan
sanya ruwa a gashi ba karamin karya gashin yake ba. Don haka sai a samo wani
abu da zai rufe kan yadda ruwan ba zai ratsa shi ba.
5.==> Yana da kyau kuma a san irin takalmin da za
a sa saboda jikewa daga ruwan sama. Ana son amfani da takalmin roba, wanda ba
zai sa a fadi ba, saboda santsin wuri a lokacin ruwan sama.
6.==> A samu kaya na mutunci wadanda za a sanya a
wannan lokacin saboda wani lokacin id an aka jike, kuma idan har tufafin wasu
matsatsu kaya ne, sai a ga surar mutum kaf ta bayyana a fili. Yana da kyau mace
ta san yadda za ta kula da kanta.
No comments:
Post a Comment