Yadda ake madarar waken soya
Assalamu Alaikum Uwargida tare da fata ana
lafiya. Waken soya wake ne wanda yake dauke da sinadarai da dama na gina jiki
da kuma kara mata lafiya. Za a iya yin wannan madarar soya din a rika bai wa
yara kanana domin yana sanya su kiba da koshi da kuma lafiya. Duk da cewa akwai
kayan abinci wadanda ake yi wa yara kanana daga wata shida zuwa biyu, waken
soya na saurin sanyasu kiba. Kowace uwa tana son ganin danta ya yi bulbul shi
ya sa a yau na kawo muku yadda ake yin waken soya din. Manya ma za su iya sha
domin kara musu lafiya.
Abubuwan da za a bukata
·
Waken soya
·
Siga
·
Flaba
·
Madara
Hadi
A jika waken soya kamar yadda ake jika wake
idan za ayi alale ko kosai amma wannan waken daban yake saboda haka, ana iya
jika shi na tsawon awa daya zuwa biyu. Sannan a sanya shi a turmi sai a kirba
shi kadan domin cire bawon da ke jikinsa. Bayan haka sai a rege shi domin gudun
tskuwa sannan a wanke waken carak!
Sannan a markada shi ya yi laushi sosai. A
sami abin tata ta kamu a tace shi sosai, sannan a sami tukunya a zuba madarar
soya a ciki, sannan a debo garin madara a kwaba da ruwa sannan a sake zuba wa a
cikin tukunyar. Sai a jira ta tafasa. Tana tafasowa za aga tana yin kumfa sai a
rika debe kumfan ana zubarwa sannan a sauke a kasa.
Sannan a zuba masa siga dai-dai yadda ake so
da kuma flaba na irin kamshin da ake so sai a gauraya har sai sigar ta narke
kuma flaba ta ji. A wannan lokacin za a iya bai wa kananan yara. Manyan kuma za
su iya sanya ta a gidan sanyi kamin a fara sha domin samun ainihin dandano mai
gamsarwa.
No comments:
Post a Comment