Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda macen da ta dara arba’in za ta yi kwalliya

Yadda macen da ta dara arba’in za ta yi kwalliya

Yadda macen da ta dara arba’in za ta yi kwalliya


Barkanmu da sake haduwa a wannan filin namu na kwalliya wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. Kwalliya aba ce da ta kamata kowace mace ta kasance tare da ita. Mata da dama daga sun dara shekara arba’in sai ka ji suna cewa sun tsufa. Ba su son yin wani abu da ya danganci kula da jikinsu. Lallai wannan babbar illa ce. Akwai al’amura da dama da matan da suka manyanta ya kamata su yi domin gyaran fatarsu da kuma jikinsu, al’amarin da ke sanyawa a cika da mamaki idan sun ambaci shekarunsu. Wannan kuwa yana faruwa ne saboda tsabagen iya kulawa da fatar jiki.

==> Ido: Ana gane tsufar mace ne daga idonta. Don haka sai a kasance cikin kula da fatar karkashin idanu. A yawaita shafa musu man zaitun a kullum idan an zo kwanciya. Yin hakan na rage yankwanewar fatar karkashin ido.

==> Gazal: Yana da kyau idan an dara shekara arba’in a kasance cikin amfani da bakin launin gazal idan an zo sanya gazal a kan gira ko kuma a cikin ido.

==> Man Shafawa: A rika amfani da nau’ukan mai masu dauke da sinadaran SPF, da ke kare fata daga kodewa. Yana da kyau mace ta rika amfani da shi kafin ta dara shekara arba’in domin hana launin fatar fuska canjawa.

==> Kumburin fuska: Idan mace ta fada cikin wadanda fuskarsu ke yawan kumburowa, sai ta rika jika kyalle a ruwan sanyi, sannan ta matse ruwan ya fita, sai ta riga shafawa a fuska har sai kyallen ya bushe.

==> Wanke kwalliya kafin kwanciya: Idan ana wanke kwalliya a kullum kafin a kwanta, yana hana yankwanewar fata, tare da hana fesowar kuraje a fuska.

==> Idan shekaru sun dan ja, yana da kyau a rika cin abinci mai kara lafiyar jiki, kamar su ganye da ’ya’yan itatuwa, domin kara wa jiki da kuma sanya fata lafiya da sheki.

==> Shafa nau’o’in mai masu kyau sosai na sanya fata ta yi sulbi da sheki. Yana da kyau a yawaita shafa mai domin hana gautsin fata da taimakawa wajen mikar da fata.


==> Dilke: Yin dilke akalla sau daya a mako na taimaka wa fata wajen yin sheki sosai.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *