Amfanin man zaitun wajen gyaran gashi
Assalamu Alaikum,
barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A
wannan makon na kawo muku bayanin yadda za ku yi amfani da man zaitun wajen
gyaran gashi. Man zaitun
na da matukar muhimmanci a jikinmu. Ana amfani da shi a matsayin man kitso.
==> Da farko a samu man zaitun mai kyau, sai a
sanya shi a murhun zamani da ake kira ‘microwabe’ ko a sanya a cikin tukunya,
sai a dora shi a murhu, sannan a bar shi ya yi dumi kamar tsawon minti 10.
==> Daga nan a rika amfani da hannu wajen dibar
man zaitun din ana shafa wa shi a karkashin gashin kai. Haka za a rika shafawa
har sai gashin ya gaurayu da man gaba daya.
==> A tabbata gashin a tsefe yake, sai a rufe
shi da hular leda kamar na tsawon minti talatin. Bayan minti talatin, sai a
wanke kan da man ‘shampoo’ da na ‘conditioner’.
Idan aka ci gaba da wanke gashin kai za a
samu canji, domin gashin zaizama mai sheki da santsi da laushi da kuma tsayi.
No comments:
Post a Comment