Yadda za a magance kaushin fata
Kaushin
fata abu ne da ke addabar fatar mutum musamman a lokacin sanyi. Akwai abubuwan
da ke sanya kaushin fata kamar yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki
da kuma jinsi. Akwai mayuka da dama wadanda ake sayar da su domin magance
matsalolin kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada. Domin bin hanya mafi
sauki wajen magance wadannan matsalolin, fata yau a Duniyan Fasaha mun kawo
muku hanyoyi tara (9) wanda zakubi wajen magance wannan matsalar suna nan
kamar haka.
1.==> A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a barshi na
tsawon mintuna biyar zuwa goma kafin a shiga wanka a kullum.
2.==> A kasance ana diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin
hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.
3.==> Za a iya kwaba fiya sannan a shafa a jiki sai a bari na
tsawon mintuna goma sha biyar sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko
kuma a hada us din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga cikin jiki.
4.==> A kasance ana amfani da man kwa-kwa a fatar jiki. A
daura man kwa-kwa a wuta ya danyi dumi sannan a mulke fatar jiki kaf dashi na
tsawon mintuna talatin kafin a shiga wanka a kwanta. A kasance yin hakan a
kullum.
5.==> Shan madara kofi daya kafin a kwanta bacci a kullum yana
taimakawa fata sosai.
6.==> A kasance ana shafa man kadanya a jiki bayan anyi wanka
da daddare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gabadaya da man kadanya
domin samun fata mai laushi mai sheki.
7.==> A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya
sannan a shafa a fuska ko fata na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da
ruwan dumi.
8.==> Lemun tsami da sukari na taimakawa wajen fitar da fatar
dake da gautsi a jiki sannan yana sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali
daya sannan a matsa ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari
na tsawon mintuna uku sannan a wanke.
9.==> Ayi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo.
Kada a maka duka a jiki yawan amfani da ababe dayawa a fata yana haifar da
kuraje a fata.
No comments:
Post a Comment