Kallon Bidiyon Batsa Na Rage Kaifin Basirar Matasa – Masana Lafiyar Kwakwalwa
Wani rahoto ya bayyana gargadin da masana
kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa suka yi cewa kallon hotuna da bidiyon batsa a Intanet
na canza kwayar halittun ƙwaƙwalwar mutane musamman ma yara da suka balaga.
Masanan sun faɗi haka ne a wani babban taron duniya da aka kammala a Rome a
kan hatsarin batsa da yara ke fuskanta a duniyar Intanet. Wani babban likitan
kwakwalwa a Amurka Donald Hilton ya yi gargadi kan mummunan tasirin da bidiyon batsa
a intanet ke yi a ƙwaƙwalwar yara.
Shugaban Katolika Fafaroma Francis ne ya
jagoranci taron na masana sama da 150 a fannin kimiya da ilimi da al’adu da
kuma kare hakkin yara kanana da aka kammala a ranar Juma’ar da ya gabata.
A wajen taron masana sun yi nazari tare da
tattauna illar kallon bidiyon batsa a ƙwaƙwalwar yara inda suka ce halayyar
ƙwaƙwalwa na canzawa a yayin da take nazari ko karatu, kuma yakan zama illa
idan aka takura ƙwaƙwalwa.
An bayyana cewa matasa na shafe lokaci suna
kallon bidiyon batsa domin ƙoƙarin gamsar da kansu ta hanyar wasa da al’auransu
da hannu a yayin da suke kallon bidiyon na batsa. Taron ya yi kira ga iyaye su
farga su lura wajen ɗaukar matakan kula da dabi’un ‘ya’yansu tare da yin kira
ga mahukunta su karfafa dokokin kare kananan yara.
No comments:
Post a Comment