Yadda za a rabu da tabon fuska
Wadanda wannan matsala ta fi shafa su ne
matasa mata da maza. Sai a ga bayan an sha wahala an rabu da kurarrajin fuska,
sai tabon ya ki tafiya. Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliyar mutum.
Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabbai. Da yawan
mutane sun gwada na’ukan mai domin rabuwa da wadannan tabbbai na fuska. Wadansu
sun yi sa’a wadansu kuma ba su yi ba. A yau na kawo muku yadda za a rabu da
wadannan tabbai na fuska. Ina so a san cewa daya za a zaba daga cikin ababen da
zan lissafo kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska.
==> A
nika itacen sandalwood, sannan a zuba zuma, a cakuda su. Sannan a shafa a
fuska ko a inda tabo yake, bayan minti 30, sai a wanke da ruwan dumi. Itacen
sandalwood na tayifar da tabo sosai kuma yana taimakawa wajen haskaka fata.
Yawan shafa zuma zalla a tabo ma na batar da shi. Amma sai an yi hakuri domin
sauki sai a hankali. Za a iya amfani da wannan hadin na tsawon wata 3 kafin
samun biyan bukata.
==> kwallon
dabino: Wannan hadin na taimakawa wajen batar da tabo musamman wanda aka
samu daga kunar wuta ko ruwan zafi. A gasa kwallon dabino a nika sannan a hada da
man kwakwa. Sai a shafa hadin a inda ake bukata. Za a iya samun kamar kwallon dabino
10 a wannan hadin.
==> A samu ganyen dogon yaro sai a hada shi da
kurkum sannan a shafa a fuska. A jira na tsawon minti 15 sannan a wanke da
ruwan dumi.
==> Za a iya samun markadadden dankalin Turawa a
shafa a kan tabo. Hakan na hana kurajen sake fitowa.
==> A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabon. Da
wari amma tana aiki sosai a kan fatar fuska ga kuma rabuwa da tabon fuska.
==> A hada karas da tafarnuwa da zuma sai a
shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.
==>
A samu ‘aking soda a hada da ruwa sai a shafa
a fuska kamar na minti 2 zuwa3. Sannan a wanke fuska.
Shin akwai yarda ake goge Zane a fuska? atemaka ga nambar whatsapp dina 08168357288
ReplyDelete