Farfesun taliyar hausa da naman kaza
Assalamu alaikum Uwargida yaya sanyi? A yau
na kawo muku yadda ake farfesun taliyar hausa da naman kaza domin magance mura
a wannan lokacin. Ina son jawo hankalinku cewa wannan irin farfesun ana iya
yinsa ga wanda ya farfado daga rashin lafiya. Kamar mace mai jego wadda aka yi
wa aiki sakamakon haihuwa da dai makamancinsu. Wannan farfesun na da armashi
sosai domin yana taimakawa majinyacin cin abinci. Sannan masu lafiya ma za su
iya shansa domin more irin sinadaren da aka girka da shi. Yana kuma taimaka wa
wajen magance mura.
Abubuwan da za a bukata
·
Bata
cokula biyu
·
Ganyen
kori
·
Yankakkiyar
karas
·
Yankakkiyar
albasa kamar rabin kofi
·
Ganyen
‘thyme’
·
Kayan
kamshi
·
Kowace
magi wadda aka yi da dandanon kaza
·
Kaza daya
·
Taliyar hausa
ko ta ‘indomie’
·
Romon kaza
·
Barkono
·
Garin
Tafarnuwa
Hadi
A wanke kaza sannan a zuba mata yankakkiyar
albasa da gishiri kadan har sai ta nuna sosai ta yi laushi. Sannan a dora
tukunya a wuta a narkar da bata sannan a zuba yankakken karas da yankakkiyar
albasa da yankakken lawashi a dan soya samasama. Sannan a zuba ganyen ‘thyme’
da magin mai dandanon kaza.
A debo romon kaza sannan a zuba a ciki har
sai ya tafasa sannan a zuba garin tafarnuwa da dakakken barkono sannan a rage
wuta sai a zuba taliyar hausa a ciki sannan a rufe na tsawon minti 20, sannan a
sauke shi da romoromonsa ana sha ana taunar namar kaza da taliya.
No comments:
Post a Comment