Lalacewar tarbiyar matasa: A ina matsalar
take?
Abin bakin ciki da damuwa game da batun
matasan kasata Najeriya. A kullum mu ake
ji Kullum sai dada lalacewa muke yi da
rashin sanin abin da muke yi. Ga rashin tabbas da rashin madogara. Ko laifin wa ye? Iyaye ko ’ya’yan ko duka?
A tawa fahimtar, duk kuwa da cewa a wajen
Huasawa karamin sani matsala ce, kuma kasancewa a kullum abin da babba ya
hango, karami ko ya hau bishiya ne ba zai iya hangowa ba, amma dai a batun
matasan nan musamman na kasata Najeriya, lallai akwai gyara da yawan gaske,
kuma akwai kura-kurai da dama da suka yi sanadiyyar wannan matsala daga
bangarorin ’ya’yan da kuma iyayen.
Lalacewar tarbiyar matasa: A ina matsalar take?
Babbar matsalar tana wajen ’ya’yan ne, amma
kuma tushen matsalar daga iyayen ne. Ya kamata mu fahimci bambanci tsakanin
kamarin matsala da kuma tushensa. Hausawa suna cewa sai bango ya tsage
kadangare ke samun damar shiga. Ashe ke nan sai iyaye sun gaza ne yaro ke samun
damar shiga wani hali, har ya fi karfin iyayen da ma al’umma baki daya. Allah
Ya kiyaye.
Tushen lalacewar matasa a yanzu daga iyaye
ne. Ina fada da babbar murna, saboda dalilai d azan zayyana.
Da farko dai wanda kuma shi ne babban dalilin
lalacewar ’ya’ya shi ne yadda iyayen suka manta ko kuma suke jahilci baban
dalilin da Allah Ya ba su ’ya’yan. Sun manta cewa Allah Ya ba su amana ne na
’ya’yan kuma zai tambayesu amanar da ya ba su. Yawancinsu sun dauka kawai su yi
aure su hayayyafa shi kenan, har za ka ji suna cewa ai Manzon Allah ma ya ce mu
yi aure mu hayayyafa. Wa ya fada Manzon Allah zai yi alfahari da sakarai ko
barawo da dan iska? Manzon Allah zai yi alfahari ne da ’ya’ya masu albarka,
wadanda da sauke nauyin da Allah Ya dora maka a kansu ta hanyar tarbiyantar da
su bin hanya madaidaiciya.
Abin ban mamaki ga irin wadannan iyayen shi
ne: Za ga gansu kullum tsaf tsaf abin ban sha’awa, za ka su yawanci suna dar
dar da cin amana. Idan ka ba su amanar dukiya ko wani abun duniya, suna kokari
su rikewa da kyau. Amma kash! Ba sa iya rike amanar Allah. Abin takaicin shi ne
yadda suke tsoron abin da mutane za su fada a game da su, amma kuma ko kadan ba
sa tsoron abin da Allah zai fada a idon dukan halittu ranar gobe kiyama a game
da amanar da Ya ba su, sannan kuma duniya su gane cewa maciya amana ne, duk kuwa
a duniya mutane suna musu kallon masu amana.
Don haka dole iyaye su gane cewa fa iyaye
amana ne, kuma Allah zai tambayesu a game da amanar da Ya ba su. Kuma babbar
amanar ita ce na ku kiyaye kanku da iyalanku daga shiga wuta. Maganar nema wa danka
aziki wannan na Allah ne. Shi yake azirta wanda ya so. Don haka babban aikinka
shi ne kiyaye iyalanka daga shiga wuta, duk abin da ya biyo baya kari ne.
Da yawan iyaye su suke fara la’antar
’ya’yansu. Zaka ga uba yana kiran dansa shege, duk kuwa da cewa shi ne ubansa.
Za ka ji uba yana kiran dansa barawo ko dan iska ko kuma ire-iren wadannan
kalaman na batanci. Wani lokacin ma za ka ji uba yana tsine wa dansa.
Shawarata a nan ita ce, idan har da gaske
muna so mu magance wannan matsalar, dole iyaye su gane nauyin da Allah Ya dora
musu. Na biyu kuma bayan tattaunawa da na yi da yawancin wadanda za ka ga sun
shiga wani hali, yawancinsu sukan nuna min cewa iyayensu ne suka tsane su, suke
kyamarsu. Don haka sai suka lura cewa kamar iyayen ba sa kaunarsu. Ke nan yadda
iyayen suke nisantar ’ya’yansa ba karamar matsala ba ce.
Yawancin iyaye ba su matsalar ’ya’yansu ba.
Kawai dai sun san sun ba ’ya’yan abinci da wajen kwana, amma wata matsalar ta
wuce matsalar wajen kwana da abinci. Yaro yana so a saurare shi ne a ji abin da
ya zo da shi, daga idan akwai gyara sai a gyara masa. Amma yawancin iyaye babu wata
alaka tsakaninsu da iyayensu sai daura fuska da zagi da fada. To a nan nake
sanar da ku iyaye: Idan ba ka jawo danka kusa da kai ba, duniya za ta jawo shi,
kuma za ta masa riga da wando.
Za ka ga yaro yana cewa bai son ubansa koda
kuwa bai fada a fili ba. Za ka yaro ya fi son uban da ya samu a wajen, wanda
watakila uban abokinsa ne ko kuma kawai ya tsince ne a gararinsa. Da nake
tattaunawa da wani yaro da aka kama ya yi sata, kuma mahaifinsa na da abin
hannu, sai ya ce min mahaifinsa ba ya ba shi kudi, kuma mahaifin nasa ne ya ce
ya bar masa gida. Koda ya bar gidan, sai ya koma gidan abokinsa da zama, kuma a
cewarsa, mahaifin abokinsa ya fi mahaifinsa sau dari, domin ko ba komai mahaifin
abokin yana tambayarsa abin da yake cikin zuciyarsa.
Wannan ko shakka babu, domin da damuwar
zuciya gara damuwar jiki. Da ka sanya mutum cikin damuwa gara ka masa duka. Da
yawan iyaye suna jefa ’ya’yansu cikin damuwa, amma ba su sani ba. Kuma idan
’ya’yan suka shiga wani hali, su ne suke fara yayata ’ya’yan a idon duniya. Za
ka wani ya ga yaro mara ji, sai ya ce wane ga danka can, sai ka ji ya ce,
wannan dan iskan ko wannan barawon. Idan ka ce masa barawo, ai ba laifi don wani
ya ce masa barawo. Idan har uba ya kira dansa barawo, to lallai duniya ma za ta
kira shi.
Sannan kuma akwai maganar auratayya. Iyaye
sukan saka ’ya’yansu cikin matsalar da ta shafi zaman auratayya da ke
tsakaninsu da matansu. Wannan shi ma babban kuskure ne. Wata yarinya take ce
min ko kadan ba ta mahaifinta saboda bay a kaunar mahaifiyarta ko kadan. Da
kyar muka mata bayani har ta dan yarda cewa yana son mahaifiyarta, amma ta dage
cewa ita kawai tsakninta da mahaifinta sai dai gaisuwa kawai. Allah Ya kiyaye. Sannan
kuma akwai matsalar kwadayi. Iyaye suna so ’ya’yansu su zama manya masu kudi,
amma kuma ba sa sauraron ’ya’yansu ko wane irin karatu suke so ko kuma wane
irin aiki suke so. Hakan ya sa suke karatu ko aikin da ba sa so kawai don ya
zama dole su yi.
Don haka nake kira ga iyaye da sanya ido a
kan ’ya’yansu ta hanyar sauraron abin da ke damun ’ya’yan. Ba wai ka sanya yaro
a makaranta bane ka ba shi abinci da wajen kwana ba shi ke nan, sai ka ce ka
sauke nauyin da Allah Ya dora maka. Dolen dole a gare ka tabbatar ka tseratar da
iyalanka daga shiga wuta. Ko ta halin yaya ne. Allah Ya bada iko.
A bangaren matasa kuma, a matsayina na
matashi, na san cewa duk matsalar ba ta wuce son abin duniya da gasa da abokai
da kuma babban matsalar, wato rashin hikima.
Abin da ya sa na ce rashin basira shi ne
kasancewar yanzu har da wadanda suke je makaranta sai ka ga sun lalace. To
akwai bambanci tsakanin ilimi da hikima ko basira. Idan Allah Ya baka ilimi ba
basira, to akwai matsala. Hikima da ilimi suke yi wa matashi jagora, amma ilimi
kawai ba hikima yakan jefa mutum ga halaka.
Matasan yanzu muna son mu yi kudi cikin
sauri, duk da cewa a nan ma akwai iyayen. Wannan ke sa wa mu ta yin gasa da
’ya’yan manya. Sannan kuma ’yan siyasa suke amfani da mu wajen bangar siyasa da
karyar cewa idan sun yi nasara, za a dama da mu. Amma da son samu nasara saisu
yi watsi da mu.
Don haka nake kira ga matasan, da mu dawo
cikin hayyacinmu. Idan muka magana da babatun cewa a bamu ragamar mulki mu ja,
to lallai ya kamata mu zama masu hankali da sanin ya kamata. Ya kamata mu rika
amfani da hikima da basirar da Allah Ya bamu wajen lura dayin abin da ya dace.
Ita dai duniya budurwar wawa ce.