yadda ake girka kazar indiyawa |
Yadda ake girka kazar Indiyawa
Assalamu Alaikum Uwargida tare da fata ana
cikin koshin lafiya. Kamar yadda na saba fada muku, yana da kyau idan za a yi
girki a rika taba birni da kauye har da kasashen waje. Hakan ya sa a yau na
dauko muku irin girkin mutanen Indiyawa ‘chicken curry’. Tare da fatan za a
gwada shi wata rana ga mai gida ko kuma ga manyan gobe domin kara ilimantar da
su a kan abincin kasashe waje.
Abubuwan
da za a bukata
·
Man zaitun
·
Albasa
·
Kori
·
Madara
(nonon da aka tafasa)
·
Gishiri
·
Dakaken
masoro
·
Heaby
cream (za a iya samu a manyan shagunan da ke sayar da kayan girke girke)
·
Kaza daya
·
Timatir
guda daya.
·
Ganyen
kori.
Hadi
A wanke kaza sannan a silala ta da kayan
kamshi da albasa da magi har sai ta yi laushi sosai. Sannan a sauke ta huce. A
sami wuka a daddatsata kanana sannan a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta
sannan a zuba man zaitun, idan ya yi zafi sai a zuba albasa sannan a yi ta
juyawa kamar na tsawon minti bakwai sannan a zuba kori kamar cokali biyu na cin
abinci, sai a ci gaba da juyawa na tsawon minti daya.
Sannan a zuba tafasashiyar madara a cikin
hadin tare da ‘cream’ da gishiri da magi da kuma yankakken timatir kanana sosai
sai a ci gaba da juyawa.
A dauko kazar da aka riga aka daddatsa a zuba
a cikin miyar sannan a rufe na tsawon minti biyu kacal sannan a sauke. Za a iya
sanya ganyen kori idan ana da bukata. A tafasa farar shinkafa sannan a dauko
hadin miyar Indiyawa a zuba a kan shinkafar tare da hada shi da jus din lemun
zaki. Hmnnn! A ci dadi lafiya!
No comments:
Post a Comment