Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka,
barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai
tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. Insha Allahu yau zamu tattauna ne game da
yar matsala wadda mutane da dama sukan fuskanta a wayoyin salulansu na Android
daga lokaci zuwa lokaci wato sakon “Insufficient Space on Device” ma’ana babu
isanshen waje a cikin waya wadda a mafi yawancin lokuta yana hana mutum tura
abu ko saukarwa daga yanar gizo.
Wasu lokutan kuma idan mutum ya duba sai ya
tarar da akwai yan wasu fili da zai dauki abubuwa da dama amma kuma yana cigaba
da nuna sakon daga lokaci zuwa lokaci wadda yakan takura wa mutum matuka idan
yanason yin aiki, a wasu lokutan ma yakan hana mutum tabuka abu.
A hakikanin gaskiya akwai ababe da dama dake
haddasa wannan matsalar wasu daga ciki sun hada da matsalar “Operating System”,
“Rashin memory card”, “Yawan Mahaja a kan waya”, “Temporary Files” da dai
sauransu.
Wasu matsaloli daga ciki suna kama da juna
misali idan muka dauki “Rashin Memory card a waya” da kuma “Yawan Mahaja” duk
sa’an da waya ta rasa memory a cikin ta to lallai duk wani abun da mutum ya tura
kama daga hoto, sauti, hoto masu motsi (video), mahaja, yana zama ne a
kwakwalwar waya haka zalika idan mutum ya fitar da mahaja a waya wadda aka fi
sani da Installing a turance shima yana zama a kan waya.
Idan muka kai duba ga dayan bangare kuma na
adana kira, sakonni da dai sauransu wayanda muka sani da wayan da bamu sani ba
duk suna zama a cikin waya ne muddin ba memory card a ciki. dalilin hakan yasa
abubuwa sukan yi wa ita wayar yawa, amma idan akwai memory a cikin ta, zai
taimaka matuka wajen adana wasu bayanai daga ciki. Yawan nuna alamar sakon
“Insufficient Space on Device” a wayar salula ba tare da daukan mataki da wuri
ba yakan haddasa babban matsala da zai shafi lafiyar wayar salulan ko kuma
yakan iya hana ta tashi gaba daya (boot) sai ansa a kwanfuta (flashing).
Wannan ya kaimu izuwa ga matsala na gaba wato
yawan “Temporary Files”, duk lokacin da mutum yayi amfani da wata mahaja a
cikin wayar Android akwai abinda ake kira da “Temporary files” a turance shi
wanna Temporary files yana Registan duk abinda mutum ya aikita a cikinsa wadda
yawansa wasu lokutan yakan kai mutuum ga wannan matslar kuma hakan na faruwa ne
idan mutum yana shiga wannan mahaja ya fita ya sake shiga wani ya fita.
Yadda Za’a Magance Matsalar Cikin Sauki
=> Da farko shawaran da zan bayar anan shine mutum yayi kokarin samar wa
wayansa memory card na musamman sannan kuma memory card din ya kasance girmansa
4 gigabyte ko yadda mutane da dama suke kira four Gib/Gig (4GB) ko kuma sama da
haka wadda farashin sa bazai wuce dubu daya (1,000) zuwa dubu biyu (2,000) ba. Mutum
daya siya wayar sama da dubu goma (10,000) rashin memory card ba uziri bane
haka zalika rashin kudin siyan memory ba dalili bane.
==> Yawan Mahaja: Tun da aka fara kirkiran
wayar salulan Android har izuwa yau da kake karanta wannan bayani ba’a yi wata
wayar salula da zata iya daukan mahajar da ake dasu ba, kimanin mahaja miliyan
60 ake dasu yau koma fiye da haka kuma ko wani waye war gari adadinsu yana kara
ninkuwa.
Saka mahaja masu yawa a cikin waya ba abun
ado bane face tara matsala wadda nan gaba zai shafi lafiyar wayar salula. Yawan
tara mahaja a wayar salula yakan kai mutum ga wannan matslar na “Insufficient
Space on Device” haka zalika yakan sa waya ta fara tafiya a hankali (slow),
yana rage ingancinsa, yana shan wutar waya (charge), yana sa waya zafi, da dai
sauransu wadda suna nan dayewa idan nace zan lissafosu dukka. Shawarata anan
shine mutum ya saka mahajar da ya tabbata zai na amafani dasu daga lokaci zuwa
lokaci sannan kuma adadin su kada ya zarce ashirin (20) ba lallai sai ya
kasance ashirin ba (20) wannan kawai shawara tace amma mutum yakan iya yin
abinda ransa ke so tunda arzikin sane. Idan kuma ya kasance mutum yana dasu
diyewa yayi hanzarin ragesu domin inganta lafiyar wayar salulansa.
==> Amfani Da Mahajar Accelerator: akwai
mahaja irin su Xmanager da Xboost wadda ake iya samun su kyauta, suna natukar taimakawa
wajen cire Temporary files da suke zaune a kwakwalwar waya, amfanin da mahaja
irin su Xmanager zai taimaka matuka wajen magance wannan matsalar cikin sauki.
Za’a kuma iya samun Xmanager ta hanyar sauke wa a yanar gizo irin su Google
Play Store da sauran kanfanoni dake bada damar saukar da mahajar Android Apps.
==> Idan har matsalar ya cigaba bayan an
saka memory card an kuma rage adadin mahaja da aka bude (Install), sannan kuma
an tabbatar babu wayansu kaya a ciki wasu nauyi kama daga hoto, sauti, hoto mai
motsi (video). Sai a bi wannan mataki.
- 1.==> Da fari aje settings na waya sanna a zabi “Apps” ko kuma “Application” ya dan gana da kanfanin wayar da mutum ke amfani dashi.
- 2.==> Za’a tura ta hannun hagu ko kuma ta hanyar zaban “All Apps” a sama kadan a hannun hagu duk dai ya dangana ne da kanfanin wayar.
- 3.==> Sai a nemi wata mahaja mai suna “Google Play store” sai a danna kai sannan a danna “Uninstall Update” sannan kuma a latsa “Clear All Data”. Bayan an kammala wayan nan matakan za’a so mutum ya kashe wayarsa ya sake kunnawa domin ganin chaji.
Wannan shine takaitaccen yadda za’a magance
wannan matslar cikin sauki, idan ana da korafi, abun cewa, ko kuma taimakawa da
wata hanya da za’a bi wajen magance wannan matsalar da bamuyi jawabi anan ba.
Za’a iya tura mana ta hanyar tuntubanmu ko kuma ta hanyar ajiyewa a comment box
da ke kasa, zamu duba sannan kuma zamu daura a kai insha Allahu muddin ya iso
mu. Allah yasa mu dace. Ameen!
No comments:
Post a Comment