Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

ABUBUWAN DA KE SA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA

ABUBUWAN DA KE SA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA

Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta}  A hakikanin gaskiya suna da yawa amma ga kadan daga ciki 

RIKO


Riko shine idan an aikatama wani laifi kabar abin a ranka ba tare da ka yafe ba uwargida ta riki maigida a xuci sakamakon wani abu ko maigida yana sa ta fita daga zuciyar miji duk sanda namiji ya yi miki wani abu yana sane ko bai sani ba to ki samu wani lokaci da yake cikin nutsuwa ko yake cikin nishadi ki nuna masa cikin tausasa harshe misali “wane kayi min kaza nasan in Allah ya yarda zai dau kuskuren shi kuma za ki kuma shiga zuciyar shi


YAWAN MITA


Yawan mita-duk macen da take da yawan mita in anyi abu baya wuce wa to zata dinga sanewa maigidanta kuma bata fiya darajaba

FUSHI


Fushi-duk mace mai yawan fushi idan sun dan samu sabani da maigida mafi yawanci da namiji idan kuka sami dan sabani in ya fita ya manta to ke ki ringa yin fushi ko ya dawo ki daura sabon fushi yana sa mace ta fita daga zuciyar namiji yana da kyau yar uwa ta dunga kai zuciyarta nesa

RASHHIN IYA GIRKI MATSALA MATA


Girki-wani ginshiki ne na sinadarin zaman aure rashin iya shi yana kawo matsala tsakanin maigida da uwar gida in dai har baya samun jin dadin abincin da uwargida ke yi har yaji abincin da zaici na waje yafi na gida dadi matsala ta faru domin yana ragewa uwargida daraja iya girki yana sa maigida yaso uwargidansa.

Idan maigida ya wadata iyalinsa da abinci to yakamata uwargida ta tsaya tsayin daka wajan ganin ta iya salo -salo na tasarinfin abinci a hakikanin gaskiya tattalin arziki yana tasiri wajan wadata komai to amma bahaushe yace da ruwan ciki wai ake jan na rijiya don haka yar uwa in dai har zaki kula da abin da maigida zai ci ba wai kullum abu daya ba ki kasance ko wane fanni na girki kin kware akwai marubuta da sukayi kokarin rubuta littafan koyon girke girke yana da kyau uwargida ta nazarci irin wadannan littafan don koyon salo salo na girki.

Duk sanda maigida ya dawo zai tarar kin gama komai na abinci sannan akwai wani sirri na girki da yawanci maigidanta suka fi so shine duk sanda yar uwa ta kawowa maigida abinci ta zauna a gabanshi yana ci kina yi mishi hira mai dadi rashin haka yana sawa mace ta fita daga zuciyar namiji.

RASHIN BAWA MAIGIDA HAKKINSA


Rashin biyawa maigida bukatarshi wajen kwanciya illah ce babba da take kawo tabarbarewar aure duk sanda maidiga zai neme ki za ki yi raki ko ki tsaya jin kunyarshi yana sa mace ta fita daga zuciyar maigida amma in har mace zata zama mai jure bukatar mijinta tare da rashin gajiyawa ko tana so ko bata so karta yadda ya gane ko da tana cikin halin (period) ne akwai hanyoyi da dama da zata gamsar da shi.





mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *