Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa

Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa

Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta} 

A wasu lokutan mukanji sunayen wasu abubuwa daga yan uwa da abokan arziki ko kuma daga yanar gizo wadda kan zamo mana sabo sabili bamu taba jinsa ba ko kuma wasu sa’an mukan ji mutane suna yawai ta ambatan sunayen, wadda a hakikanin gaskiya bamu sansu ba balle mu san yadda suke aiki. 

Kalmar Hosting kan zama abu sabo ga wasu haka zalika yakan zama al’amuran yau da kullum ga wasu. Shin menene ma’anar wannan Kalmar?

Menene Hosting? 


Akan kirasa da “Hosting” ko kuma “Web Hosting”. Hosting wata fasaha ce dake bawa kanfuna da kuma mutane damar saka ko daura shafuka na rubutun ra’ayin kai a yanar gizo wadda aka fi sani da “Blog” ko kuma “Website” a turance. Wadda hakan ke baiwa maziyarta damar samun abinda suke bukata ta hanyar amfanin da wayoyin salula ko kuma kwanfuta tare da taimakon data. 

Shafukan yanar gizo (Blog/Website) suna zama ne a wasu na’ura na musamman wadda ake musu lakani da ‘Servers’ a turance. Duk sa’an da mutum ke son ziyartan wani shafi a yanar gizo; abinda zayyi shine rubuta addereshin shafin misali https://duniyanfasaha.guidetricks.com a cikin browser sannan ya latsa ma dannin ‘Enter’ ko dai ‘Go’ a wayar salaula ko kuma a kwanfuta a daidai wannan sa’an na’uran da mutum ke amfani dashi zai shiga duniyar yanar gizo sannan ya nemo addreshin da mutum ya saka ta hanyar samo kanfanin da me shafin  yayi amfanin dashi wajen ragistan shafinsa sannan ya nuna wa mai ziyartan. 

Yawancin kanfuna masu kula da wayan nan na’ura na hosting wadda ake kira da “Web Host” sukan bukaci mutum ya samo addreshinsa na musamman wadda aka fi sani da “Domain” a turance domin akwai bukatan hakan kafin daura wani shafi a yanar gizo. Idan har ya kasance mutum bayi da shi sukan iya taimaka ta hanyar jagorantar mutum yadda zai siya cikin sauki.       

Me Ake Nufi Da Web Host Ko Kuma Web Hosting Provider?


‘Web Host’ ko kuma ‘Web Hosting Provider’ a turance, wani harka ne da mutane keyi wajen sarrafa fasaha wadda ke taimakawa shafukan yanar gizo yin cikakken aiki da ake bukata. 

Ta wani bangaren zamu iya cewa 'Web Host' ko kuma 'Web Hosting Provider' wasu kanfuna ne da ke kirkiran fasha da kuma na’uran da ake bukata wajen daura shafuka na rubutun ra’ayin kai wadda hakan ke baiwa mutane damar ziyartan shafi tare da taimakon wayar salula ko kuma kwanfuta.

Menene Amfanin Shi Wannan Hosting?


Hosting wadda a wasu lokutan a kan kirasa da “Web Hosting” a turance, yana amfanine da wani fasaha na musamman tare da hadin gwiwar ita kwanfuta, yana taimakawa matuka ta hanyar samar da wasu fili a duniyar yanar gizo wadda ke bada damar daura shafi na rubutun ra’ayin kai a ciki, wadda yin hakan zai bawa mutane damar ziyartan shafin a kowani sako a cikin fadin duniya ta hanyar amfani da yanar gizo.    

Ire-Iren Hosting


A gaskiya hosting ya kasu izuwa sassa daban daban amma a yau zan zayyano wadda akafi amfani dasu a duniyar mu na yanzu wasu daga ciki sun hada da: 

==> Karamin Hosting (Small Hosting Services): Wannan ne na farko daga ciki jerin kashi na hosting. A wannan shirin akan baiwa mutum damar daura shafinsa a yanar gizo amma a kayataccen farshi sannan kuma yana da matukar iyaka. A wannan shirin mutum yakan iya daura shafinsa na kai ko kuma na kasuwanci wadda bashi da nauyi sosai.      
 Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa
==> Babban Hosting (Large Hosting Services): Wanna Tsarin yakan baiwa kanfanoni da dama daura shafinsu a yanar gizo. Ba lallai sai kanfanoni kadai ke amfani da wannan tsarin ba, mutane masu babban shafuka sukan iya yin amfani da wannan tsarin soboda girmansa da kuma ingancinsa. 

Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa
Wannan shine takaitaccen bayani game da hosting, amfaninsa da kuma ire iren sa. A wasu makonni masu zuwa insha Allahu zamuyi bayani game da ire iren web hosting service da kuma kashi kashi na hosting wadda yasha banban da wayan da mukayi bayani a yau. 

Karanta: Muhimmancin Ilimin Computer – Kowa ya iya allonshi ya wanke 1


Shin kana/kina da tsokaci ko Karin bayani game da abinda mukayi jawabi a kai yau? Za’a iya ajiyewa a wajen sako na kasa wato comment box ko kuma ta hanyar tuntubanmu a shafukan sadarwa ko dai hanyar daya dace.  


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *