Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Abubuwa Goma (10) Da Ke Haifar Mana Da Ciwon Koda

Abubuwa Goma (10) Da Ke Haifar Mana Da Ciwon Koda

Tare Da Muhammad Abba Gana (Jikan Marubuta)

Ciwo daga Allah ne haka zalika magani daga Allah ne, Allah yakan daura wa mutum da yaso ciwo ba wai dan baya kaunarsa ba, fa che dan ya jarraba imaninsa da kuma hakurinsa. Haka kuwa ta dayan bangaren domin Allah bai daura maka komai ba hakan baya nufin cewar yafi sonka fiye da kowa ko kuma kai na musamman ne a garesa.

Amma a mafi yawancin lokutan akwai ababe bila adadin da muke aikatawa wadda hakan ke haifar mana da babbar illa ta gangaren lafiyar mu. Koda a jikunmu yakan iya kasancewa tamkar Carburetor a jikin mashin, mota, jirgi, janarator ko kuma wani launi na karfe makamancin haka.

Suna da matukar amfani ta bangaren lafiya domin suna taimakawa ta hanyar dakatar da datti daga wucewa gaba wadda rashin hakan kan iya haifar da babban matsala. A duniyar mu ta yau mutane da yawa suna fama da matsalar ciwonta wadda ba lalli kowa ne yasan mukaddashin faruwan hakan ba a wasu lokutan kuwa muna sane dasu amma saboda rashin kulawa muna cigaba da aikatawa.

Koma dai ya abun ya kasance insha Allahu yau a Duniyar Fasaha zamu zayyano wasu daga cikin manya-manyan matsaloli dake janyo hakan da kuma yadda zamu kiyaye domin kubutar da kanmu daga kamuwa da ire-iren cututtukannan.

1.==> Yawan Rike Fitsari: Ina aiki, ina aji, banson zirga zirga, ina jin kunyar fita ko tambayar wajen bahaya, ina reno…. Wasu daga cikin dalilai da muke badawa a koda yaushe kenan ta wannan bangaren wadda hakan ke sanya mu rike fitsari na tsawon lokuta masu yawan gaske ba tare da sanin illar yin hakan ba. Yawan rike fitsari na wasu lokuta kan gajiyar da ita koda da kanta sannan yakan kuma iya gajiyar ko dakatar da wasu abubuwa dake aiki a mafitsarin dan adam wadda hakan ke haifar da wasu cuttutuka irin su yoyon fitsari da dai sauransu.

2.==> Rashin Shan Ruwa Akan Lokaci: Wannan yana daya daga cikin abubuwan da ke haifar da wannan babbar matsala domin kuwa duk lokacin da koda yake aiki yakan bukaci ruwa domin taimaka masa wajen gudanar da ayyukan daya saba, sai sa yana da kyau a koda yaushe idan jiki ya bukaci ruwa ayi kokarin samar masa ba tare da jigina hakan da wasu dalilai ba.

3.==> Yawan Shan Barasa Ko Kwayoyi: Ba wani addini daya inganta shan barasa ko kuma kwayoyi masu yawa saboda illolin dake tattare da su. Yawan shan kwayoyi ko barasa yakan gigita wasu bangarorin jiki ta hanyar ninka adadin ayyukan da zasu iya yi wadda hakan ke haifar da babbar matsala ga ita koda da wasu sassa na jikin dan adam. 

4.==> Yawan Shan Kaya Masu Dauke da Sinadarin Caffeine (Kamar Goro, Tabar Wiwi, Cofee): Kusan za’a iya cewar ire iren wayan nan sinadaran wasu lokutan sukan yi aiki a jikin dan adam tamkar kwaya wadda hakan ke sanya yawan gudun wasu sassa na jiki ba tare da shiri ba.

5.==> Yawan Amfani Da Gishiri: Da yawan mutane za’a ga suna yawan zambadan gishiri tamkar abinci mai dadi a wasu lokutan kuma wasu suna daukansa kamar wata abin adone ko birgewa ta hanyar shan sa haka ko kuma ta hanyar sanya sa sosai a cikin abinci ba tare da sanin illolin dake tattare dashi ba. To lallai a kiyaye sosai domin yin hakan zai iya janyo babbar matsala ga lafiyar jikin dan adam wadda zai iya kaiwa ga matsalar cutar koda.

6.==> Rashin Magance Matsalolin Sanyi: Tabbas ciwon sanyi babbar matsala ne ga lafiyar jikinmu wadda a mafi yawancin lokutan ana samunsu ne ta hanyar jima’i, kazantar baki ko kuma yawo cikin danshi ba tare da takalmi ba, idan wannan cutar ta dade a jikin dan adam ba tare da magance sa akan lokaci ba hakan zai iya kaiwa ga cutar ciwon koda.

7.==> Shan Taba: A duk lokacin da aka ga wani kayan karfe na yawan hayaki to tabbas akwai matsala tattare dashi haka zalika ta bangaren dan adam yawan zukar hayaki babbar matsala ne domin yakan rage wa’adin wasu sassa na jiki sannan kuma yakan haifar da wasu matsalolin manya kamar: sankarar Huhu, Sankarar Zuciya da kuma koda, ire iren wayan nan cututtukan basu cika nuna alamu ba sai lokacin da suka kare aiki wato lokacin da suka cinye gaba daya, sai sa a koda yaushe masana kiwon lafiya ke tsawatar wa game da busar hayaki.  

8.==> Abinci Masu Dauke Da Sinadarin Protein: Wayan nan sun hada da kifi, nono, kwai da sauransu. Ba ina nufin daukansu ke kawo wannan cutar ba fa che yawan cinsu lokaci zuwa lokaci. Wadda kusan daya ne a kowani bangare na rayuwa. Yawan daukan abinda ya zarce adadi yakan janyo matsala ga lafiyar jiki.

9.==> Amfani Da Magungunan Kashe Zafin Ciwo Wato Analgesics: Saboda ingancinsu da kuma karfinsu yawan amfani da ire-iren wayan maganungunan kan haifar da kwayoyin cututtuka irin su ciwon koda.

10.==> Rashin Samun Isashen Barci: Saboda neman duniya ko neman suna mukan salwartan da daren mu wajen yin wasu ayyuka wadda hakan ke haifar mana da babbar matsala ga lafiyar jiki, domin a duk lokacin da jikin dan adam bai samu hutu ba ‘Koda’ yakan gaji sannan sai ya fara kumbura hakan ke haifar da ciwon koda sannan kuma ya shafi wasu sassa na jiki wadda ke janyo matsaloli bila adadin.

Wasu daga cikin manyan abubuwa da mukeyi kenan wadda ke haifar mana da ciwon koda, Allah shi kiyayemu daga ire iren wayannan cututtukan. Shin akwai wasu abubuwan da mukeyi wadda ke haifar mana da wannan cutar da bamuyi bayani a nan ba za’a iya bada gudumawa ta hanyar rubuta mana a comment box dake kasa ko kuma ta hanyar tuntubanmu a hanyoyin sada zumuntan mu na facebook, twitter da kuma whatsapp.  



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *