Assalamu Alaikum yan uwa barkan
mu da war haka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabo shirin namu wanda
yake zuwa muka kai tsaye daga mujallar Duniyar Fasaha, Insha Allahu yau zamu
koyi yanda ake goge sakon da ake tura bisa kuskure koda kuwa ya isa wajen wanda
aka tura wa.
A
yan kwanakin da suka shude kamfanin WhatsApp tayi nasaran fitar da wani hanya
ta yanda zai taimaka wa mutane wanda suke amfani da dandalin sadarwan ta wajen
share sakon da suka tura bisa kuskure koda kuwa ya isa wurin wanda ake so a
tura wa.
Shi wannan hanyar da aka masa lakani da “Delete for everyone” ma’ana “share wa kowa” yana aikine a kowace waya mudin mayar tayi nasaran daukan WhatsApp. Zaka iya goge sakon da ka tura bisa kuskure zuwa ga wani ko kuma a group. A gane wanna yana aikine kadai a dandalin sada zumuta na whatsapp.
Shi wannan hanyar da aka masa lakani da “Delete for everyone” ma’ana “share wa kowa” yana aikine a kowace waya mudin mayar tayi nasaran daukan WhatsApp. Zaka iya goge sakon da ka tura bisa kuskure zuwa ga wani ko kuma a group. A gane wanna yana aikine kadai a dandalin sada zumuta na whatsapp.
Yanda
akeyi
Misali
na tura sako zuwa ga wani abokina sai dai ma’anar bata cika ba bisa yan wasu
kuskure da na tafka yayin saurin rubutu in har hakan ta kasance da kai abunda
zakayi/kiyi shine ka/ki danna kan rubutun ka/ki tsaya ma’ana ka/ki latsa kan
rubutun da aka tura nayan wasu daki kai.
Zai
fito ma ka/ki da wasu zabi guda shiga wanda suke bayyana a sama wajen suna ko
lambar mutum
Dan
share sakon sai a latsa wannan mabullin wanda yayi kama da akwatin zib da shara”Delete
button” wanda shine na hudu a jiren ababen da suka bayyana. Wasu lokutan baya
bayyana a wajen yakan canza mazauni in har ba ka/ki gansa inda na ambata ba sai
a latsa wannan ma bullin na karshe wanda a jiki dot guda uku za’a ga an rubuta “Delete”
sai a latsa kai.
Za’a
ga an rubuta “Delete for me” ma’ana “goge wa kaina” amfanin wannan mabullin
shine in harka ka/ki dannan kai sakon da ka tura ko aka turo ma zai bace ma kai
kadaine amma mutumin da ya turo ko ka/ki tura masa zaigani sai dai in har shima
ya danna, sai na biyun waton “Cancel” shi wannan mabullin amfanin sa shine soke
abunda ka zaba in dai ka latsa wannan zai mayar da kai izuwa shafin baya ba tare
da yin wani aiki ba. Sai na karshen wanda shine manufar wannan darasin wato “Delete
for everone” shi wannan mabullin in har ka latsa sa toh abunda ka tura zai bace
ma’ana kai da ka tura da wanda ka turawa gaba dayan ku bazaku ga idaninsa ba ya
tafi Kenan.
Dan
takaiceciyar hanaya Kenan da za’a bi wajen goge sakon da aka tura bisa kuskure
a whatsapp in ka/ki na da Karin bayani ko naiman taimako zaka/ki iya rubutawa a
akwatin da ke kasa.
No comments:
Post a Comment