Yadda
macen da ta dara arba’in za ta yi kwalliya
Barkanmu da sake haduwa a wannan filin namu
na kwalliya wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha.
Kwalliya aba ce da ta kamata kowace mace ta kasance tare da ita. Mata da dama
daga sun dara shekara arba’in sai ka ji suna cewa sun tsufa. Ba su son yin wani
abu da ya danganci kula da jikinsu. Lallai wannan babbar illa ce. Akwai al’amura
da dama da matan da suka manyanta ya kamata su yi domin gyaran fatarsu da kuma
jikinsu, al’amarin da ke sanyawa a cika da mamaki idan sun ambaci shekarunsu.
Wannan kuwa yana faruwa ne saboda tsabagen iya kulawa da fatar jiki.
==>
Ido: Ana gane tsufar mace ne daga idonta. Don
haka sai a kasance cikin kula da fatar karkashin idanu. A yawaita shafa musu
man zaitun a kullum idan an zo kwanciya. Yin hakan na rage yankwanewar fatar
karkashin ido.
==>
Gazal: Yana da kyau idan an
dara shekara arba’in a kasance cikin amfani da bakin launin gazal idan an zo
sanya gazal a kan gira ko kuma a cikin ido.
==> Man
Shafawa: A rika amfani da nau’ukan mai masu dauke da sinadaran SPF, da ke
kare fata daga kodewa. Yana da kyau mace ta rika amfani da shi kafin ta dara shekara
arba’in domin hana launin fatar fuska canjawa.
==>
Kumburin fuska: Idan mace
ta fada cikin wadanda fuskarsu ke yawan kumburowa, sai ta rika jika kyalle a
ruwan sanyi, sannan ta matse ruwan ya fita, sai ta riga shafawa a fuska har sai
kyallen ya bushe.
==> Wanke kwalliya kafin kwanciya: Idan ana
wanke kwalliya a kullum kafin a kwanta, yana hana yankwanewar fata, tare da
hana fesowar kuraje a fuska.
==> Idan shekaru sun dan ja, yana da kyau a rika
cin abinci mai kara lafiyar jiki, kamar su ganye da ’ya’yan itatuwa, domin kara
wa jiki da kuma sanya fata lafiya da sheki.
==> Shafa nau’o’in mai masu kyau sosai na sanya
fata ta yi sulbi da sheki. Yana da kyau a yawaita shafa mai domin hana gautsin
fata da taimakawa wajen mikar da fata.
==> Dilke: Yin dilke akalla sau daya a mako na
taimaka wa fata wajen yin sheki sosai.