Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Amfanin ayaba ga fatar jiki

Amfanin ayaba ga fatar jiki
Amfanin ayaba ga fatar jiki

Assalamu Alaikum Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku cikin sabon shirin namu wanda ke zuwa muka a babban zauren nan na Duniyan Fasaha insha Allahu yau zanyi bayanine game da amfanin ayaba ga fatar jikin dan adam, ayaba yana daya daga ciikin sanannun yayan itatuwa wayanda muke cinsu yau da kullum amma sai dai bamu san wani irin amfani yake dashi a jiki ba, wasu lokutan ba kawai ana cinsa saboda jin dadi bane ko kuma saboda ana da kudi illar sinadarin dake dauke dashi.  
A baben da muka yi magana a kansu wadanda suka shafi kwalliya, ayaba na daya daga cikin ababen da ba mu yi magana akanta ba. Don haka ne a yau na dauko ayaba domin a san irin sinadaren da take dauke da su, da kuma yadda za a yi amfani da ita wajen gyaran fata. Ayaba na dauke da sinadaren bitamin C kuma tana taimakawa wajen fitar da sabuwar fata a lokacin da fata taji rauni. A sha karatu lafiya.

·        Ayaba na magance cizon kudan cizo a jiki. Kudan cizo na yi wa fata lahani sosai. Don haka, sai a samu ayaba a shafa a wajen da aka yi cizon.

·        Idan an fadi akan keke fata ta dan kwarzane, sai a samu bawon ayaba a shafa a wajen. Ayaba na taimakawa wajen warkar da wajen, ba tare da barin wani tabo ba.

·        Ayaba na taimakawa wajen sanya hakoranmu haske; bayan an wanke baki da magogi, sannan a samu bawon ayaba a goga akan hakori. Idan ana yin haka na tsawon makonni biyu za a ga cewa hakoran sun kara haske.

·        bawon ayaba na warkar da irin kwarzanen da ake samu a wajen soshe- soshen fata.

·        Masu yawan kurajen fuska da na jiki, sai a samu bawon ayaba a riga shafawa a fuska da jiki a kullum kafin a kwanta barci. Washe gari sai a wanke. Za a ji sauki a cikin kwanaki kadan.

·        Ko an san cewa bawon ayaba na magance ciwon kai? A samu bawon sannan a daura a inda kan ke harbawa na tsawon mintuna talatin (30) za a ji sauki.

·        bawon ayaba na magance kaikayin fata. A shafa bawo n a kan kurajen.

·        Ayaba na taimakawa wajen haskaka takalmanmu. Ko za a gwada ne sannan a ba ni labari. Bayan an goge takalmi da tsumma sannan a dauko bawon ayaba a goga a jikin takalman za a ga takalmin ya fara sheki.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

3 comments:

  1. WOW just what I was looking for. Came here
    by searching for medicine

    ReplyDelete
  2. na gwada kuma naji dadi allah kara ilimi

    ReplyDelete

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *

Blog Archive