Kek
din wake
Assalamu Alaikum Uwargida tare da fatan kuna
lafiya da kuma cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin Kek din
wake.
Kayan hadi
·
Wake
·
Sukari
·
Bakin hoda
·
Kwai
·
Bota
Yadda ake yi:-
farko uwargida za ki samu wake mai kyau sai ki
barza a inji. Idan aka kawo sai ki bakace domin duk bawo da bakin da ke jikin
waken ya fita. Idan kika tabbatar ya gyaru sosai sai ki bayar akai miki inji a
nika shi ya yi laushi sosai. Sanann sai ki tankade. Sai ki ajiye a gefe daya.
Sannan ki samo mazubin da za ki kwaba kek din a ciki sai ki zuba sukari da bota
ki juya su sosai sanan ki kawo kwai ki fasa akai, ki ci gaba da juyawa. Idan
kika tabbatar ya biyu. (anan wasu suna amfani da injin na mider wanda hanya ce
da take da sauki da kuma kyau wajen kwabin kek) sannan sai ki dauko garin
wakenki ki zuba tare da bakar hoda akan wancna kwabin sai ki ci gaba da juyawa
kamar yadda ake yi wa fulawa. Idan kika gama sai ki dauko mazubin kek din ki
shafa masa man bota a jiki sannan ki zuzzzuba kullun a ciki. Sannan sai ki jera
su a abin da kike yin gashi da shi. Ki barshi na kimanin minti 20. Idan ya gasu
za ki ji yana kanshi.
Good job!! can i share this in my blog ?
ReplyDeleteGood job!! can i share this in my blog ?
ReplyDelete