Assalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon Shirin namu na lafiya wadda yake zuwa muku kai tsaye daga shafin Duniyan Fasaha, Insha Allahu yau zamu maida dubane ga abinda ake kira da Dabino a hausance. Dabino na dauke da sinadarai na ban mamaki, sinadaran da ke da matukar muhimmanci ko dai wajen samar da waraka daga wata cuta ko kuma na hana kamuwa da wata cuta ko kuma inganta wasu sassa na jikinmu ta yadda za su gudanar da ayyukansu na yau da kullum daidai wa daida yadda kuma ya kamata.
Wasu daga cikin sinadarai sun hada da:
A kowane giram dari (100) na
layayyen dabino ana iya samun:
- Fiber – giram 6.7
- Potassium – giram 696
- Copper – miligiram 0.4
- Manganese – miligiram 0.3
- Magnesium – miligiram 54
- Vitamin B6 – miligiram 0.2
Wadannan sinadarai na da matukar muhimmanci ga layarmu. Misali: Bitamin B6 din da ke cikin dabino na taimakawa wajen kara wa mutum bukatuwa da abinci tare da bude masa ciki musamman ma ga wanda ya dade bai ci abinci ba.
Shi yasa ma Manzon Allah (S.A.W) Ya ke cewa:
idan daya daga cikinku ya yi azumi to ya yi buda baki da dabino, amma idan bai
samu ba, to ya yi amfani da ruwa, domin ruwa na tsarkakewa. Abu Dawud Ya
ruwaito shi a hadisi mai lamba 2348.
Dabino yana dauke da sinadarin dake karawa jiki kar da kwari. Dabino na saisaita sukarin da ke cikin jinin mutum wanda yake raguwa sakamakon rashin cin abinci ko sha. Dabino yana dauke da sinadarin iron wanda yake taimakawa wajen karin Jini sannan yana karfafa jini da hantar mutum.
Wadanan jawaban su suka sa muka
gane abinda ke boye ta fadin Manzon Allah (SAW) akan Hadisin da muka kawo na
sama. Bayan tarin magunguna da Dabino ke magancewa.
Ga wasu daga cikin Amfanin Dabino
- Yana samar da ruwan jiki
- Yana taimakawa mata masu ciki
- Yana kara ruwan nono
- Yana maganin matsalar fata
- Yana maganin ciwan kirji
- Yana maganin ciwan suga
- Yana maganin ciwon ido
- Yana gyra matsara
- Yana maganin Basur
- Yana magance matsalar Rashin banci
- Yana kara laar jariri
- Yana rage kiba wacce bata laa bace
- Yana maganin majina
- Yana karfafa kashi
- Yana maganin ciwon hakuri
- Yana maganin Gymbon ciki (ulcer)
- Yana kara kar da nauyi
- Yana maganin tsutsar ciki
- Yana maganin ciwo ko yanka
- Yana karawa koda laa
- Yana maganin tari
- Yana maganin kullewar ko cheshewar ciki
- Yana rage kitse
- Yana maganin cutar Daji (cancer)
- Yana maganin Asthma
- Yana kara karn kwakwalwa
- Yana ciwon baya, ciwon gabbai, ciwon sanyi, wanda yake kama gadon Baya.
- Yana kara sha’awa da kuzari
- Yana magance cutuka dake damun kirji
- Yana karya sihiri.
No comments:
Post a Comment