A
hakikanin gaskiya fuska na daya daga cikin wuraren daya kamata a kula dashi
sosai domin da zarar an hangi mutum itace abinda za a fara kalla. A mafi yawancin
lokuta mutane su kanyi korafin yadda fatar fuskarsu ke chanza launi a yan wasu
kankanin sa’a ba tare da sanin silar faruwan hakan ba.
Akwai abubuwa bila
adadin dake sa hakan wayanda sun hada da yawan shiga rana, yawan shafe-shafen
man kam fani, yawan goge fuska da kaya masu karfi, yawan saka kayan kwalliya a
fuska wadda hakan ke rufe kofofin shigar iska da dai sauransu.
Insha
Allahu yau a Duniyar Fasaha zamu zayyano yan wasu hanyoyin da za’abi wajen kula
da fatar fuska cikin sauki.
A
hakikanin gaskiya wanke fuska daga lokaci zuwa lokaci yana da matukar tasiri. ba
wai lallai sai za’ayi wanka ko alwala kadai ba yana da kyau ko da bacci za’a
kwanta a wanke fuska sosai saboda yana saukar da zufa, datti, da dai sauran
ababen da ke iya zama a kai wadda hakan ke toshe kofofin shigar iska sannan ya haifar
da wasu matsaloli kamar:
- Janyo Kyasbi a fuska
- Janyo Maruru a fuska
- Yana rage kyau musamman ga mace
- Janyo Tabo da dai sauransu
Mata
da dama ba su damu da yin wanka da daddare kafin su kwanta barci ba. Wata ma
tun kwalliyar da ta yi da daddare ta fita hira wajen saurayinta haka za ta
shigo gida ta kwanta barci ba tare da ta wanke fuskarta ko kuma ta yi wanka ba.
Haka
zalika idan aka koma dayan bangare na maza wani idan yayi wanka da safe ya fita
nema bayan ya dawo ga gajiya ga ansha rana sannan ya kwanta zubur kamar buhun
albasa ba wanka ba hamdala. Don haka ya kamata mu canza gaba daya, mu rika
wanke fuskarki mu daga lokaci zuwa lokaci domin yin hakan yana da babbar fai’da
ga lafiyar jikin mu. Wasu daga cikin sun hada da:
-
Wanke fuska ko wanka kafin a kwanta na
sanya kwanciyar hankali, yana sanya isaka ta ratsa kofofin fuska mai kyau wadda
hakan ke sanya barci mai dadi.
-
Idan mutum ya kwanta ba tare da wanke fuska
ba, mayukan da ya shafa a fuskarsa na taruwa sannan a wasu lokutan suke sanya
fitowar manyan kuraje, wadda sai an yi da gasken gaske kafin a rabu da su.
-
Yana da kyau a wanke fuska da sabulun wanke
fuska mai kyau, domin fuska ba ta cika kwari ba kamar sauran bangarori na ji ba.
Yayi kau
ReplyDelete