Assalamu Alaikum Warahamatullahi Uwargida da
fatan kina cikin koshin lafiya da farin ciki Allah yasa haka amin. A yau na
kawo muku yadda ake yin Pazza da kuma kayan hadi a shakaratu lafiya.
Kayan hadi
·
Filawa
·
Gishiri
·
Yis
·
Man zaitun
·
Manshanun
kanti (Cheese)
·
Mayonnaise
·
Kayan
kamshi
·
Tumatir da
farar albasa da koren tattasai
·
Tsokar kaza
Yadda
ake yi:-
Da farko za a jika yis da ruwan dumi kamar
tsawon minti 10, sai ki zuba gishiri da man zaitun. Sannan sai ki kara filawa a
cikin wannan ruwan yis din ki kwaba har sai ya yi tauri. Idan ma kika ji shi ya
yi ruwa ko lauashi sosai sai ki kara fulawa don yayi tauri.
Daga nan sai ki
rufe ki bar shi ya hau zuwa mintina 30. Idan ya hau (kumbura) sai ki sami
farantin gashi ki juye filawar a ciki sannan ki sanya a cikin oben ki gasa ki
bar shi tsawon mintuna biyar.
Ana sai ki yanka tumatir da farar albasa da
koren tattasai kanana. Sai ki koma wurin fulawarki ki duba idan ta gasu sai ki
fito da ita. Sannan ki dauko kayan tumatir din da kika yanka sai ki zuzzuba
akai da dan garin kayan kamshi ki barbada. Sai ki sami tsokar naman kazarki da
kika yanka kanana tare ki zuzzuba akai.
Sannan sai ki kawo mayonnaise ki
yaryada akai. Sai ki zo ki rufe samansa da manshanun kanti (chease). Sanann ki mayar
cikin abin gashin (oben) don ya kara gasuwa. Za ki ji yana kamshi sosai sai ki
fito da shi daga ciki shi ke nan Pizza ta yi sai ci.
No comments:
Post a Comment