Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Za Ki Hada Kazar ‘Chicken Balls’

Yadda Za Ki Hada Kazar ‘Chicken Balls’

 

Kayan Hadi


  • Kaza
  • Kwai
  • Dankalin Turawa
  • Magi da gishiri
  • Tattasai da attarugu da albasa
  • Man gyaxa
  • Kori (Curry)


Hadi

Idan uwargida ta wanke kazarta tas, sai ta tafasata da dan gishiri da albasa har sai ta yi laushi sosai, sannan a cire kasusuwan da ke jikin kazar.

A dafa dankalin Turawa ya dahu sosai sannan a ajiye ta a gefe. A markada tattasai da attarugu da albasa.

Bayan haka, sai a tsoma dafafen dankalin tare da kazar a cakuda su da maggi da gishiri da kuma kori (curry).

Sannan a fasa kwai a kan hadin da aka yi. Sai a mulmula su daya bayan daya. Sannan a dora man gyada a wuta a tukunyar suya a soya su. Bayan ya soyu sai a sauke. Chicken balls ya yi ba karya, aci dadi lafiya!.mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *