Assalamu alaikum jama’a, a yau na zo muku da yadda ake hada jus din kankana.
Za a iya yin shi domin sayarwa ko kuma domin sha a gida ko biki.
Kayan Hadi
- Kankana
- Sukari
- Madara
- Flavor
Yadda ake hadawa
A yanka kankanar a zuba ta a blender a markada ta sosai ta yi sumul babu sauran gudajin kankana.
A tace markadaddiyar kanakar sosai sannan a zuba sukari daidai bukata a ciki.
Daga nan sai a zuba madarar ruwa da flavor cikin chokali a cikin kankanar da aka tace sannan a jujjuya.
Idan an gama sai a sa a fridge a bari ya yi sanyi ko kuma a sa kankara a ciki gwargwadon yadda ake so a sha.
Yadda ake hadda ‘kankana jus’ cikin sauki
ke nan, da fatar za’a jarraba.
No comments:
Post a Comment