Yadda Ake Yin ‘Yam Balls’ A Saukake
Jama’a barkan mu da wannan lokaci, a yau za mu nuna yadda ake yin kwallon doya da kywai (yam balls) a gida a saukake.
Ana iya yin ‘yam balls’ a matsayin abinci don marmari, tarbar baki ko sana’a.
Kayan Hadi
- Doya
- Attarugu
- Albasa
- Kwai
- Magi
- Gishiri
- Kori
- Mai
Yadda Ake Hadawa
Da farko za a fere doya a yanka ta sai a wanke a sa a tukunya a dora a wuta da dan gishiri a bari ta nuna.
Idan ya nuna sai a sauke a kawo turmi mai tsafta a daka doyar sama sama.
Sai a dauko jajjagen attarugu, albasa, magi da kori a zuba a kan doyar a juya su hadu sosai.
Daga nan sai a rika dunkula doyar a yi ta kamar kwallo.
Sai a fasa kwai a dora kasko a wuta a sa mai.
Idan man ya yi zafi sai a rika dauko kwallon doyar ana sawa a kwai ana soyawa a man.
Idan ya yi sai a kwashe.
Yadda ake yin yam balls ke nan, da fatan za a jaraba a gani.
No comments:
Post a Comment