Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Ake Hada Abun Wanke Bayan Tukunya

Yadda Ake Hada Abun Wanke Bayan Tukunya

Ayau mun kawo muku yadda ake hada abun wanke bayan tukunya (vim) a gida cikin sauki.

Ana kuma amfani da shi wajen wanke butar karfe ko goge duk wani abu mai tsatsa.

Ana fi amfani da shi wajen wanke bayan tukunya ne saboda yana fitar da tsatsa da bakin tukunya sosai.

Abubuwan Da Ake Bukata:

  • Bawon kwai
  • Toka
  • Omo

 

Yadda Ake Hadawa

Da farko za a samu bawon kwai wanda ya bushe sosai a daka shi sosai a tankade.

Sai a samu toka shi ma a tankade sai a hada da tankadaden bawon kwan.

Sannan sai a zuba omo kadan a juyaya sosai.

Wannan shine yadda ake hada vim a gida.

Da fatan zaa gwada a gani.mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *