Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

YADDA ZAKA MAGANCE SHANYEWAR MB AKAN WAYAR KA NA ANDROID

YADDA ZAKA MAGANCE SHANYEWAR MB AKAN WAYAR KA NA ANDROID TARE DA MUHAMMAD ABBAGANA

YADDA ZAKA MAGANCE SHANYEWAR MB AKAN WAYAR KA NA ANDROID



Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. Insha Allahu yau mun kawo muku hanyoyi da zaku bi wajen magance matsalar shan yewar data ko mb a wayar salula na android.  

To a hakikanin gaskiya akwai ababe da dama wanda suke sanya wayar android shan data ko megabyte amma manyan daga cikin su sun hada da Google Play store, saukar da application mai bude kansa wanda ke amfani da yanar gizo, ko kuma yakan iya zama updating da wasu application keyi na kansu muddin sun shunshuni yanar gizo.

Koma daga ina matsalar take ga hanyoyi da zaku bi wajen magance wannan matsalar. Abun kula nan shine ko wace waya yana da hanyar shan data amma dai kashi casa’in bisa dari suna faruwa ne bisa hanyoyi dana ambata a baya ga kuma yanda za,a magance matsalar.

Cikaken hanyoyi da zaka bi wajen wagance shanyewar data, mb ko megabyte a wayar salulanka na android.

Mataki na Farko, Dakatar da Application daga Updating kansa: akwai application da dama wanda akowani karshen wata ana da’da musu abubuwa sabbi a ciki wanda kafin mutum ya samu damar aiki da wannan sabin ababen dole sai yayi updating na application dinsa. Sai a wasu lokutan Muddin wayar android ya sami data a bude baya tambayar mutum ko yana bukatar sabon update sai dai kawai ya saukar masa a cikin wayar sa na salula wanda hakan ke janyo karewar data.

Dan magance wannan matsalar akwai hanyoyi da dama wanda mutuum zai iya bi amma mafi sauki daga cikin hanyoyin shine dakatar da updating application daga settings na Google Play store, dan dakatarwa sai mutuum ya shiga Google Play store Application >> sai yaje zuwa ga ‘settings’>> sai ya zabi “Auto Update Apps” sannan mutum sai ya kuma zabi na farko wanda aka rubuta “Do not auto-update apps” ma’ana kar yayi updating wani application. Wannan shine hanya mafi sauki wajen magance application da ke updating kansa.      

YADDA ZAKA MAGANCE SHANYEWAR MB AKAN WAYAR KA NA ANDROID TARE DA MUHAMMAD ABBAGANA


Mataki na Biyu, Dakar da Google Play store daga aiki ko kuma Application masu aiki in sun sami data a bude:  Google play store gidane da babban kamfanin nan na google ke kula dashi wanda ke baiwa mutane damar saukar da application a wayar salulansu, saukar da application a waya dai yana cin yan wasu mb.

Duk lokacin da wannan application din yake aiki ko yana bude akwai wasu yan chargi da ake ma mutuum haka zalika ba lallai sai mutuum ya bude da hannunsa ba yakan iya fara aiki da kansa wanda hakan ke janyo karewar data ko mb a wayar salulan mutum.

Dan dakatar da Google play store na wayar ka sai ka ziyarci ‘settings’ na wayarka >> sannan sai aje izuwa ga >> ‘Application’ ko ‘Apps’ ya dangana da yanda yake rubuce a wayar>> sannan sai mutum ya zabi “All apps” ko kuma mutuum ya zabi “All application” to anan mutum sai ya nemi>> “Google Play Store” a jerin application da suke wayar bayan mutum ya samu sai ya shiga akwai akwa tuna biyu wanda aka tanadar sai a latsa na biyun wanda ke dauke da “Force Stop” ma’ana dakata daga aiki> zai tambayeka shin ka tabbatar kana son Dakar da wannan application din sai ka zabi ‘Ok’ ma’ana eh. Shikennan anan an magance matsalar shan data ko mb wanda google play store keyi.

YADDA ZAKA MAGANCE SHANYEWAR MB AKAN WAYAR KA NA ANDROID TARE DA MUHAMMAD ABBAGANA


Za,a iya bin hanya daya gabata wajen magance shanyewar data da wasu application keyi amma lokacin da mutuum yazo zaban application mai makon ya zabi “Google Play store” sai ya zabi application da yake tunanin yana yawan bude kansa.

Mataki na karshe, Dakatar da sync settings na wayar salulanka: dan dakatar da syn settings na wayar salula ga mata kan kamar haka kaje izuwa ga "Settings" Ka dan tafi can kasa, sai ka zabi "Account and sync settings" Ka cire zabin da ke kan "Background data". Ka maida shi babu zabi, zasu yi maka gargadi, kawai ka manta da su, ka cire alamar zabi.


Insha Allahu za,a samu saukin shanyewar mb ko data Allah yasa mu dace


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *