Girkin koda
Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da
fatan ana lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka koda. Akwai hanyoyi da
dama wadanda mata ke sarrafa koda. Walau a gasa ko a girka. Nawa salon girkin
daban yake. Don haka yana da kyau a kasance an karanta wannan shafin domin gano
sirrin girki da kuma canza salon girki a kodayaushe, domin yara su rage kwadayi
a makwafta.
Abubuwan da za a bukata
·
koda
·
Albasa
·
Tumatir
·
Garin
tafarnuwa
·
Magi kori
·
Garin
citta
·
Attarugu
·
Man gyada
·
Koren
tattasai
Hadi
A wanke koda ta fita tas. Sannan a yayyankata
kanana, sai a sanyata a cikin tukunya tare da zuba mata ruwa kadan. Sannan a
rufe. Idan ya fara nuna sai a yayyanka albasa da yawa a ciki da zuba yankakken
tumatir da magi da garin tafarnuwa da kuma garin citta kadan sosai. Sannan a
rage wuta sai a shiga gaurayawa. A zuba man gyada kadan sai a cigaba da juyawa
har sai albasa da tumatar da kuma attarugu sun nuna. Sannan a kwashe a sanya a
kwano.
Sai a yayyanka danyen albasa da koren tattasai a zuba a kan kodar domin
kawata girkin. Za a iya cin wannan girkin da dafadukar shinkafa ko kuma farar
shinkafa da jus din lemun zaki. A ci dadi lafiya.
No comments:
Post a comment