Kwai na daga cikin abincin da mutane kan ci musamman domin marmari ko kayatarwa mai hanyoyin sarrafawa iri-iri, ciki akwai awarar kwai.
Mutane da dama na son cin awarar kwai ko su yi da kansu, amma ba su san yadda za su bullo wa abun ba.
Ku kwantar da hankalinku, yau a Duniyan Fasaha mun kawo muku cikakken bayani yadda ake yin awarar kwai cikin sauki.
Abubuwan Da Ake Bukata:
- Kwai
- Nama
- Mai
- Maggi
- Attaruhu
- Albasa
Yadda Ake Hadawa
A gyara nama mara kitse a markada shi sannan a jajjaga attarugu da albasa a juye a ciki.
A fasa danyen kwai sannan a kada shi sai a sa masa magi da gishiri da sauran kayan hadi daidai bukata a juya shi sosai.
Daga nan dan a hada kwan da naman a motsa, sannan a juye hadin a cikin farar leda sai a saka a tukunya a dafa kamar alala.
Idan ya nuna sai a sauke a yayyanka kamar awara.
Daga nan sai a sake kada danyen kwai a rika tsoma hadin da aka riga aka dafa a ciki ana soyawa.
Wannan shi ne yadda ake hadda awaran kwai.
A ci dadi lafiya.
No comments:
Post a Comment