Assalamu alaikum, tare da fatar ana cikin koshin lafiya.
Kamar yadda mutum ke son cin abinci mai dadi, yakan so ya samu abun sha mai dadi da kayatarwa da zai hada da shi ko ya sha shi haka a matsayin abin marmari.
Don haka a yau mun kawo muku yadda ake hada yadda ake hada jus din karas wato ‘carrot juice’.
Kayan Da Ake Bukata
- Karas
- Sukari
- Madara
- Flavour
- Lemon zaki
Yadda Ake Hadawa
Za a wanke karas a fere shi sannan a yanka shi kanana.
Daga nan sai a sanya a blender a markada shi ya yi laushi.
A tace shi sosai yadda ba za a samu gari ko tsaki-tsakin karas ba.
A yanka lemon zakin a matse ruwansa a tace sannan a ajiye a gefe.
Azuba wa tataccen karas din madara da flavor daidai bukata da kuma sukari sai a juya.
Daga nan sai a dauko ruwan lemon a zuba a ciki a motsa.
Shi ke nan sai a sanya hadin a cikin fridge, idan ya yi sanyi a sha shi yadda ake bukata.
Wannan shi ne yadda ake hadda karas juice a takaice.
No comments:
Post a Comment