Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Hanyoyin Kula Da Fatar Fuska Cikin Sauki

Hanyoyin Kula Da Fatar Fuska Cikin Sauki


A hakikanin gaskiya fuska na daya daga cikin wuraren daya kamata a kula dashi sosai domin da zarar an hangi mutum itace abinda za a fara kalla. A mafi yawancin lokuta mutane su kanyi korafin yadda fatar fuskarsu ke chanza launi a yan wasu kankanin sa’a ba tare da sanin silar faruwan hakan ba. 

Akwai abubuwa bila adadin dake sa hakan wayanda sun hada da yawan shiga rana, yawan shafe-shafen man kam fani, yawan goge fuska da kaya masu karfi, yawan saka kayan kwalliya a fuska wadda hakan ke rufe kofofin shigar iska da dai sauransu. 

Insha Allahu yau a Duniyar Fasaha zamu zayyano yan wasu hanyoyin da za’abi wajen kula da fatar fuska cikin sauki.

A hakikanin gaskiya wanke fuska daga lokaci zuwa lokaci yana da matukar tasiri. ba wai lallai sai za’ayi wanka ko alwala kadai ba yana da kyau ko da bacci za’a kwanta a wanke fuska sosai saboda yana saukar da zufa, datti, da dai sauran ababen da ke iya zama a kai wadda hakan ke toshe kofofin shigar iska sannan ya haifar da wasu matsaloli kamar:

-  Janyo Kyasbi a fuska
- Janyo Maruru a fuska
- Yana rage kyau musamman ga mace
- Janyo Tabo da dai sauransu

Mata da dama ba su damu da yin wanka da daddare kafin su kwanta barci ba. Wata ma tun kwalliyar da ta yi da daddare ta fita hira wajen saurayinta haka za ta shigo gida ta kwanta barci ba tare da ta wanke fuskarta ko kuma ta yi wanka ba.

Haka zalika idan aka koma dayan bangare na maza wani idan yayi wanka da safe ya fita nema bayan ya dawo ga gajiya ga ansha rana sannan ya kwanta zubur kamar buhun albasa ba wanka ba hamdala. Don haka ya kamata mu canza gaba daya, mu rika wanke fuskarki mu daga lokaci zuwa lokaci domin yin hakan yana da babbar fai’da ga lafiyar jikin mu. Wasu daga cikin sun hada da:

-         Wanke fuska ko wanka kafin a kwanta na sanya kwanciyar hankali, yana sanya isaka ta ratsa kofofin fuska mai kyau wadda hakan ke sanya barci mai dadi.
-         Idan mutum ya kwanta ba tare da wanke fuska ba, mayukan da ya shafa a fuskarsa na taruwa sannan a wasu lokutan suke sanya fitowar manyan kuraje, wadda sai an yi da gasken gaske kafin a rabu da su.
-         Yana da kyau a wanke fuska da sabulun wanke fuska mai kyau, domin fuska ba ta cika kwari ba kamar sauran bangarori na ji ba.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

1 comment:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *