Shaukin so
Yadda bege yake, to kusan
haka shima shauki yake, sai dai kuma ba daya suke ba, kowanne yanada da nasa
tsarin.
Shi shauki shine mutum ya
dinga jin wani irin farin ciki da annushuwa, da wani yanayi mai faranta rai a
duk lokacin da yaga, ko yaji muryar masoyinsa.
Shauki, wani nau’ine a
cikin so da ke haifar da farin ciki ga masoya, wanda ke wanzuwa tamkar daddadan
sanyin iskar yammaci a lokacin zafin rana. Idan so ya kai so, to dole a samu
wadannan abubuwa kamar haka:
·
Kauna da soyayya
·
Aminci da yarda cikin soyayya
·
Yarda da wanka ake so a cikin zuciya
·
Mallakawa wanda ake so, so zalla
·
Gaskatawa da wadda kake so a rai
·
Tabbatarwa zuciyarka soyayya zalla
·
Begen masoyiya ko masoyi
·
Shauk’in soyayya a cikin zuciya
Don haka shi shauki,
masoyi ko masoyiya zasu dinga jin wani tsantsar farin ciki da annushuwa na tare
da walwala da duk lokacin da suka ga junansu.
Ko
kuma a duk lokacin da masoya suka ji muryoyin junansu, koda kuwa a wayar salula
ne, to sai ka ga fuskokinsu sun nuna alamar farin ciki da walwala a Zahiri. A
lokacin da jikin mutum yayi zafi, ba zafin rashin lafiya ba.
Ya
kasance ace ana zafine, mutum na gumi, to zaka ga mutum yana bukatar ya dan
samu inuwa mai sanyi ya zauna a ciki, har ma yayi barci idan yaji dadinta. Ko
kuma ace mutum ya samu ruwa mai sanyi ya watsa a jikinsa don ya gusar da wannan
zafin da ya addabe shi.
To
kamar haka ne ga masoyin da yaga masoyinsa yake ji a cikin ransa, wani dadi ya
ratsa shi har yaji ya manta da duk wata damuwa, sai farin ciki ya mamaye
zuciyarsa.
§ Shauki
tamkar shakar daddadan kamshi turare ne a cikin hanci
§ Shauki
tamkar shakar kamshin furen fulawa ne a yayin da iskar yammaci mai dauke da
ni’imtaccen yanayi ba wanzuwa a sararin duniya.
§ Shauki,
tamkar dandanon zazzakar tattaciyar zuma ne a baki.
§ Shauki,
wani yanayi ne mai gusar da damuwa a zukatan masoya.
§ Shauki
wani bangare ne dake samar da walwala a gurin masoya
§ Shauki,
wani yanayi ne wanda kan haifar da tsatsar farin ciki ga masoya.
§ Shauki,
wani irin abune mai kasancewa a yayin da so ya zamo tamkar jini a jikin masoyan
da suke kaunar junansu.
No comments:
Post a Comment