Babu
shakka kayan kwalliya na taimakawa matuka wajen bunkasawa da kuma kara fito da
kyanki. Kai kayan kwalliya irin na zamani ba kayata kyau ba ma har kawar da
muni suke yi. Zan iya cewa irin kayan kwalliyan da ake da shi yanzu da wadanda
ake kirkira a kullum, amshin addua ne ga masoya kwalliya a duk fadin duniya.
Sai
dai akwai matsala. Sau daya yadda muke amfani da kayan kwalliyan kan iya
haifarwa fatarmu matsalar da kayan kwalliyan ko dubu nawa ba za su iya rufewa
ba. Insha Allahu yau Duniyan Fasaha ta kawo muku hanyoyi guda uku (3) da ake
amfani da kayan kwalliya wadanda fata da ace tana da baki da ta koka:
1.==> Kwana da kwalliya a fuska: A
lokacin da muke barci ne jikinmu ke aiki tukuru wajen kawo karshen matsalolin
da sassan jikinmu ke fuskanta, ba’a bar fata a baya ba. A yayin da muka kwanta
barci da kwalliya, hakan baya samuwa domin kuwa kayan kwalliya na yin kane kane
a cikin kofofin fata su hana ruwa gudu. A dan haka sinadaran da zasu karawa
fatarmu inganci, kyawu da sheki ko dai daga wani mai da muka shafa akan fatar
ko kuma wanda jikinmu ya sarrafa daga abinci ba zasu iya yin amfaninsu ba yadda
ya kamata.
Idan
mutum mai saurin samun kuraje ne, hakan yakan kawo su da gaggawa, idan ma ba
kya yin kuraje to tabbas za ki tashi daga barci kiga fatarki ta rasa shekinta
da kyawunta. Ci gaba da yin hakan zai tabbatar da lalacewar fatarki a nan gaba.
Ki tabbatar kin wanke kayan kwalliya tsaf daga fatarki, daga su har kamu
kamunsu kafin ki yi barci da daddare dukkuwa irin gajiyar da kika yi.
2.==> Amfani da kayan kwaliyan da
irinsu bai dace da irin fata ba: Idan fatarki tana da
maiko, ki ka je kika sayi kayan kwalliya masu tushe mai maiko, toh kinyi amfani
da kudinki kin jibgawa kanki aiki, gani da yadda suke da matukar tsada ma a
yanzu ya sa ya cancanta ayi maki jaje. Dalili kuwa shine maimakon ki kara kyau,
da kin shafa sai fuska ta cika da maiko.
Banda
toshe kofofin fata da kayan kwalliyan sukayi, ga kuma maiko ya zo ya kara na
shi akai. Hakan yana haifar dawa fata matsala matuka.
Haka
kuma idan kina da busasshiyar fata kika fara amfani da kayan kwalliya marasa
maiko, nanma fa akwai matsala domin kuwa fatarki zata yi ta bushewa har ta fara
yamushewa ta zama kamar ta tsohuwa. Banda hakan ma, wani lokaci irin sinadaran
da ke cikin kayan kwalliya masu hatsari ne ga lafiyar fata, shi yasa za gi ga
yawanci an rubuta cewa ki dan gwada kadan a matse matsin gwiwar hannunki na
tsahon awanni kafin ki fara amfani da shi. Amma da yawanmu bama yin hakan. Sai
an gama shan kyau, fata kuma ta zo ta zama kamar taswirar Nijeriya, a zo ana
cewa an samu ‘skin reaction’ da ba’a san dalilin sa ba.
3.==> Amfani da kayan kwalliyan
da suka tsufa: Brushes din da ake amfani da su wajen yin
kwalliya da bakin kayan kwalliya na matsawa irin su foundation gurin taruwar
kwayoyin cuta suke zama. Shi yasa aka shawarci ma’abota kwalliya da su tabbatar
cewa ko da yaushe sun ajiyesu a guri mai tsabta, sun kuma tabbatar da ba’a hada
amfani da su da kowa ba.
Ban
da haka ana so a daina amfani da mascara guda daya bayan wata 3, shi kuma
foundation bayan shekara daya. Idan basu kare ba kawai zubar da su ake. Brushes
kuma za’a iya wanke su a cikin ruwan zafi domin kashe kwayoyin cutar lokaci
lokaci. Ajiye kayan kwalliyan nan a cikin jaka daya su hada datti su hada datti
ba alkahairi bane ga fatarki, wani lokacin ma har kaisu baki ake yi wanda anan
ma zasu iya kwaso matsala daga yawun baki. Ya kamata dai a kiyaye, domin ni fa
na fi son naga kowa tsaf tsaf, fata na sheki kamar wancan abun da na manta
sunashi.