Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Hanyoyi Guda Biyar Da Ake Magance Basir Cikin Sauki

Hanyoyi Guda Biyar Da Ake Magance Basir Cikin Sauki

Basir yana samuwa ne a lokacin da jijiyoyin da ke mafitar bahaya suka kumbura daga ciki ko daga waje (wanda muke kira basir mai tsiro), wanda yawancin lokuta hakan na faruwa ne a sakamakon wahala wajen fitar da bahaya. Basir yafi matsawa wadanda ke da matsalar jinkiri wajen narkewar abinci a ciki, masu ciki da kuma tsofafi.

Duk da dai wannan matsala ba ta haifar da wata barazana ga rayuwar mutum, rashin dadin da take haifarwa ya kan matsawa mutane sosai har su ta shan magunguna barkatai, wanda akarshe ba lallai bane hakan ya zama alkhairi a garesu. Mujallar Duniyan Fasaha ta kawo muku hanyoyin magance wannan matsala guda biyar masu matukar sauki wadanda suka kunshi abubuwan da muke amfani da su na yau da kullum.

1.==> Man zaitun

Man zaitun ba’a barshi a baya ba wajen magance basir domin kuwa yana taimakawa matuka wajen kara laushi da kuma taushin jijiyoyin da ke hanyar fitar da bahaya wanda hakan na rage wahalar da ake sha matuka. Ana shan cokali daya ko biyu na man zaitun tare da abinci a kowace rana domin ganin alfanunsa.

2.==> Man Kwa-Kwa

Ana shafa man kwakwan ne a gurin kumburin akai akai idan basir din na waje ne, banda ragen radadin ciwon da hakan yake yi, za’a ga girman shi ya fara raguwa a cikin ‘yan kwanaki.

3.==> Aloe Vera

Aloe vera yana taimakawa wajen kawar da radadin basir a cikin lokaci kalilan. Ana amfani da shi ta hanyoyi guda biyu: ko dai a matsa ruwan a shafa a gurin kumburin ko kuma a yayyanka ganyen a fere kayoyin sanna a sanya shi a firiji ya daskare, sai ana dorawa akan kumburin. Hakan yana taimakawa matuka wajen motsar da kumburi.

4.==> Leman Tsami

Shima leman tsami ana amfani da shi ta hanyoyi guda biyu. Ana hada ruwan shi da citta da kuma zuma a na sha, sannan kuma ana shafa ruwan leman tsamin a waje. Hakan yana magance kumburin da ya ke daga ciki da kuma wanda yake daga waje, ya kuma magance radadi.

5.==> Kankara

Ana fasa kankara a kunshe ta a cikin tsumma mai tsafta, sannan ana dannawa akan kumburin. Hakan yana kawo saukin ciwon sosai kuma ya rage kumburi.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *