Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Sabon tsarin MTN na samun data bisa farshi mai rahusa

Sabon tsarin MTN na samun data bisa farshi mai rahusa

Assalamu Alaikum yan uwa barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mujjalar Duniyan Fasaha. Yau mun taho muku da wata hanya da zaku bi wajen samun Mb mai sauki daga kamfanin MTN. wanda hanyar ta fara aiki ne a yan wasu kwanaki da suka shude.

MTN yana daya daga cikin manya kuma sannanne kamfani wanda yake taimakawa wajen sada zumunta ta hanyar kira, sako ko kuma ta hanyar ziyartan shafukan yanar gizo. Sannan yana daya daga cikin kamfanin dake da saurin network a ko ina a cikin fadin kasar nan (Nigeria).

A yanda kowa dai ya sani in zaka sayi Mb bisa tsarin kamfanin MTN Da naira N100 suna bada Mb ashirinne (N20) ne amma daga bisani anyi nasarar samun sauyi daga kamfanin wanda yanzu ana bada Mb 50 ko kuma 75, sannan kuma na naira dari biyar (N500) ana bada Mb 250 ko kuma Mb 500 haka zalika na dubu daya ana bada Mb dubu daya 1000 ko kuma dubu da dari biyar 1500 wanda yake bada damar shiga ko wani irin shafi a duniyar yanar gizo.


A wannan makon kamfanin MTN ta fitar da wani salo wajen samun Data mai yawa bisa farshi mai rahusa. Wanda da naira N100 za’a sami Mb har dari biyu da hamsin 250 sannan kuma da naira 200 za’a sami Mb dubu daya 1000 sai kuma na karshen da naira dubu daya za’a sami Mb dubu hudu. Domin samun wannan garabasar sai a latsa *559*65# sannan a zabi tsarin da ake bukata a cikin ukun dana lissafo a baya. Abun kula!! Wannan garabasar ba lallai ne yama aiki ba yana aiki ne wa mutane na musamman, amma yana da kyau a jarraba.  


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *