Kayan marmari Ko kun san cewa duk abubuwan da
suka kunshi ya’yan itatuwa na da muhimmanci a wajen gyaran jiki? Akwai ’ya’yan
itatuwa ko kwallonsu da ke karrama kwalliyar mace ko namiji. Don haka ne a yau a
Duniyan Fssaha muka kawo muku. Domin idan akwai wadanda suke son magance wata matsalar
fata ko na son sanya murya zaki ce, za su san irin yadda za su magance
matsalolinsu.
==>
Domin zakin murya
Za a samu ganyen mangoro sai a tafasa ruwan a
rika sha kullum domin samun zakin murya. Akwai matan da suna da babbar murya da
in sun yi magana sai a zata namiji ne, wannan na iya magance musu matsololinsu.
Za a iya shan wannan ruwan sau biyu ko uku a rana.
==>
Domin kunar fata
A samu kwallon dabino kamar kwallo 10 sai a
gasa, sannan a daka ya yi laushi. Bayan haka, sai a samu man kwakwa a hada
garin kwallon dabino da ita. Sai ana shafa wannan maganin a inda aka kone.
==>
Domin magance hurhurar ka
A samu ganyen kori da ganyen aloe bera da
ganyen lalle. Sai a daka su tare a wuri daya. Bayan an yi hakan, sai a shafa a
gashi mai furfura. Sannan sai a jira na rabin awa kafin a wanke. Yana da kyau a
yi amfani da wannan hadin kamar sau uku zuwa hudu (3-4) a mako.
==>
Domin samin fata mai laushi
Samu nutmeg da madara ba yan an nika nutmeg
din, sannan sai a zuba madara a ciki. Sai a shafa a jiki kullum kafin a yi
wanka. A bari ya bushe a fatar jiki kafin a wanke. Yin hakan kullum na sanya
fata sulbi.
No comments:
Post a Comment