Idan
aka hada wadanna hanyoyi da kuma shan magani to da izinin Allah za’a samu
saukin matsalar basir a cikin kankanin lokaci. Wadannan hanyoyi sun hada da:
·
Gaggauta fitar da bahaya a lokacin da aka ji shi ba tare da
jinkiri ba
·
Shan ruwa a kai a kai
·
Yawaita cin kayan lambu da kayan itatuwa
wadanda ke taimakawa wajen narkar da abinci da wuri su kuma sanya bahaya yayi
laushi ya fita
ba tare da matsala ba.
·
Yawaita motsa jiki da gujewa zama a guri
daya na tsahon lokaci
·
Gujewa zaunawa a yayin fitar da bahaya kamar yadda
ake yi a yawancin bandakuna na zamani. Zama yana hana rage saukin fitar bandaki ya kuma
ta’azzara basir. Tsugunne irin na iyaye da kakanni yafi alkairi
·
Zama a guri mai Laushi a ko da yaushe
·
Da fatan wadannan hanyoyi za su taimaka
wajen rage basir din ya addabin al’ummar hausawa.
No comments:
Post a Comment