Assalamu Alaikum Warahamatullahi Uwargida da
fatan kunanan lafiya cike da koshin lafiya da farin ciki ya lafiyan yara da
kuma mai gida ya dawiniyar yau da kunlu Allah Unbangiji ya musu da alkarri ya
kuma karamusu kwarin giawa amin. A yau Uwargida na kawo muku yadda ake sarafa
Lemon Masara da kuma kayan hadihadi sa yadda zakiyi hadin a shakaratu lafiya.
Kayan hadi:
·
Masara
·
Kwakwa
·
Sukari
·
Madara
·
Filebo
Yadda ake yi:
Da farko uwargida za ki samu masara danya sai
ki cire ta daga jikinta, sai ki dafa ta. Idan ruwan ya huce sai ki markada ta
sannan ki tace. Sai ki sami kwakwarki ki cire bayanta sannan sai ki goga ta
sannan ki markada ta ki kuma tace. Idan kika kammala tacewa sai ki sami mazubi
ki juye dukkanin ruwan kwakwar da na masarar a ciki sannan sai ki sami madarar
ruwa ki zuba. (amma ana iya sa madarar gari) sai ki dauko sukari ki zuba a
ciki. Sannan ki sa a cikin na’urar sanyaya abubuwa ta firinji. Idan ya yi sanyi
sai a dauko a sha.
No comments:
Post a Comment