Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Illolin Saka Takalma Masu Tsini – Gareku Mata

Illolin Saka Takalma Masu Tsini – Gareku Mata

Akwai jerin wasu mata da ke ganin saka takalma masu tsini yana daga cikin ado musamman ga ya mace ba tare da sannin illoli dake tattare dashi ba. 

Da akwai kuma jerin wasu mataye da ke ikirarin cewar duk ya mace da ba ta saka takalma masu tsini to fa lallai wannan yar bata cika goma ba.

Tura Zuwa:

Amfanin Nonon Akuya Guda 8 A Jikin Bil Adama

Amfanin Nonon Akuya Guda 8 A Jikin Bil Adama

Amfanin Nonon Akuya Guda 8 A Jikin Bil Adama


Premium Times ta rawaito cewa hukumar bada shawara akan bunkasa ayyukkan noma na Najeriya NIFAAS ta yi kira ga mutane da su yawaita shan nonon akuya saboda kara lafiyar jiki da yake yi.

Hukumar ta bayyana cewa Nonon Akuya yafi na saniya amfani a jiki.

Tura Zuwa:

ILLOLIN TALLA GA RAYUWAR ƳA MACE

ILLOLIN TALLA GA RAYUWAR ƳAN MATA

Sana'ar talla tana da illoli masu ɗunbun yawa ga rayuwar mata musamman wanda sun munzalin yin aure. 

A mafi akasin garuruwan jihohin Arewacin Najeria, yana wuya kayi tafiyan minti guda baka ga ƴan mata suna talla ba; a bakin kasuwa ko makaranta, tasha ko masana'anta, wureren leburori ko kan titi, gidajen kallon kwallo ko sinima, filin kwallo ko gidajen dambe.... babu dare babu rana.

Tura Zuwa:

Kula da fata a lokacin sanyi

Kula da fata a lokacin sanyi

Kula da fata a kowane lokaci yana da matukar muhimmanci, sai dai a lokacin sanyi fata tana bukatar kulawa ta musamman saboda yaushi ko yamutsewa da tsattsagewar da fatar kan yi sakamakon busawar iskar hunturu. Ga wasu hanyoyi wadanda za su taimaka wajen kare fata daga tsattsagewa a lokacin sanyi:­-

Kula da fata a lokacin sanyi


1.==> Shan ruwa mai yawa. Amfanin shan ruwa ga jikin dan adam yana da yawan gaske. Duk da cewa a lokacin sanyi mutane ba su fiye son shan ruwa ba, amma hakan babbar hanya ce wajen taimaka wa fatarsu ta kasance tana sheki tsawon lokacin hunturu. An so mutum ya sha ruwa kimanin lita biyu zuwa uku a rana. Sai dai wannan bai hada da shan shayi ba, a maimakon haka an so mutum ya yawaita shan lemo.

2.==> A yawaita shan kayan itatuwa da kuma ganyayyaki wannan zai sa fata shekki da walwali.

3.==> Idan an tashi wanka a yi da ruwan dumi. Duk da an san cewa a lokacin hunturu ana bukatar ruwa mai zafi musamman idan da safe za a yi wankan, sai dai ya zama wajibi anan a kaucewa yin amfani da ruwan zafi saboda yana haifar da yamutsewar fata da kuma kaikayi. An so mutum ya yi wanka da ruwa marar zafi sosai kuma wanka ya kasance na dan takaitaccen lokaci, ma’ana kada ya wuce tsawon mintuna biyar zuwa goma wajen wanka.

4.==> Ana so a rika yawaita goge jiki ‘scrubbing’ wannan shi zai sa duk wata matacciya da busasshiyar fata ta fita tare da ba wa sabuwar fata wuri don tofowa.
5.==> Shafa mai akan lokaci, mun san yadda jiki yake saurin bushewa saboda kadawar iska. A duk lokacin da aka yi wanka yana da kyau a shafa ma tun a bandaki lokacin da dan ragowar danshi a jikin fatar.

6.==> A zabi mai da ya dace da lokacin sanyi, ma’ana mai wanda ke da maiko wanda zai sa fata ta kasance cikin danshi na tsawon lokaci. Duk wani mai da zai zama ya sa fata tauri ba shi da amfani a wannan lokaci na sanyi. A wannan lokaci amfani da man kadanya ko man zaitun yana taimakawa fata kwarai da gaske.


7.==> Haka kuma akwai bukatar mutum kada ya manta da labbansa da kuma hannuwansa, kasancewar wadannan wurare suna da muhimmaci a jikin dan’adam kuma sanyi yakan yi musu illa don haka akwai bukatar koda yaushe mutum ya kasance yana tare da man lebe da kuma wani mai na hannu mai ruwa-­ruwa.
Tura Zuwa:

Yadda Za Ki Kula Da Gashinki Lokacin Sanyi

Yadda Za Ki Kula Da Gashinki Lokacin Sanyi

Kowane bangare na jikin bil adam yana neman kulawa na musamman domin kara masa kargo da kuma inganchi amma akwai wasu wajajen da suke bukatar kulawa na matuka, gashi na daya daga cikin wayan nan waja je, komin karanchin sa komai yawansa gashi yana bukatar wankewa lokaci zuwa lokaci ba w yadda wasu suka kasance sunayi ba, da sabulun wankin gashi wanda ya dace da irin gashin da kike dashi (za a ga bayanin haka a rubuce a jikin sabulun) Duk da cewa mata ba su fiye son karanta jikin ba haka zalika wasu basu fiye wanke gashinsu ba saboda gudun kada ya zube, amma akwai bukatar akalla yaga ruwa ko sau daya a cikin makonni biyu.


Tun kafin a wanke gashin, idan akwai amosani, ya kamata a kankare shi sosai, haka zalika masu kazzuwa da kuma kaska yana da kyau a sami magani don kada sai an wanke ya rika tasowa yana bata gashin. Sannan akwai bukatar a nemi maganin amosani, kaska na musamman.


Bayan wanke gashi sai a bar shi ya ya sha iska na yan masu mintuba, ba a son taje jikakken gashi domin yin hakan yakan haifar da wata matsala, sannan sai a shafa masa mai wanda ya yi dai dai da gashin. Idan kitso kika fi so, bayan kin wanke kin shafa masa mai sai ki rangada wanda kike so akan lokaci ba sai yayi tsami ba. 

Wato a barsa bayan an wanke har tsawon mako guda ko fiye da haka ba tare da anyi kison ba haka zalika kada ya wuce makonni biyu ba tare da kin kwance ba. Idan kuwa baki son kitso, a kullum dole ne ki zauna ki taje gashin tare da shafa masa mai daya kamata, sannan sai ki daure shi da madaurin gashi (Ribbon) dai dai yadda kike so.

Idan da hali, Zai yi kyau duk bayan wata daya kije salun ki yi masa abin da ake kira steaming, wannan ne zai hana shi zubewa. Idan kuma ke mai sha’awar yi wa gashi shamfo ce (retourching) shi ma akwai bukatar ki rika maimaitawa a duk bayan watanni biyu. Idan kuma gashinki mai karfi ne za ki rika yi kamar sau daya a wata.


Yawan yin shamfo a cikin kwanakin da suka gaza wata guda, masana sun ce akwai yiwuwar zubewar gashi saboda yawan kone shi da ake yi. Bayan duk kin gama wadannan akwai turaren gashi da za ki rika feshe gashin ki da shi, don ya rika sa shi kamshi na musamman kuma ya kamata ki sani cewa mayukan da ya yi wa wata aiki ba lalle ya yi miki ba, kowa da kalar sa haka zalika kowa da kallar fatarsa don haka ki kula sosai wajen zabar wanda zai dace da naki gashin.
Tura Zuwa:

Hanyoyin Kula Da Fatar Fuska Cikin Sauki

Hanyoyin Kula Da Fatar Fuska Cikin Sauki


A hakikanin gaskiya fuska na daya daga cikin wuraren daya kamata a kula dashi sosai domin da zarar an hangi mutum itace abinda za a fara kalla. A mafi yawancin lokuta mutane su kanyi korafin yadda fatar fuskarsu ke chanza launi a yan wasu kankanin sa’a ba tare da sanin silar faruwan hakan ba. 
Tura Zuwa:

Yadda ake hada Pizza

Yadda ake hada Pizza

Assalamu Alaikum Warahamatullahi Uwargida da fatan kina cikin koshin lafiya da farin ciki Allah yasa haka amin. A yau na kawo muku yadda ake yin Pazza da kuma kayan hadi a shakaratu lafiya.

Kayan hadi

·     Filawa
·     Gishiri
·     Yis
·     Man zaitun
·     Manshanun kanti (Cheese)
·     Mayonnaise
·     Kayan kamshi
·     Tumatir da farar albasa da koren tattasai
·     Tsokar kaza

Yadda ake yi:-

Da farko za a jika yis da ruwan dumi kamar tsawon minti 10, sai ki zuba gishiri da man zaitun. Sannan sai ki kara filawa a cikin wannan ruwan yis din ki kwaba har sai ya yi tauri. Idan ma kika ji shi ya yi ruwa ko lauashi sosai sai ki kara fulawa don yayi tauri. 

Daga nan sai ki rufe ki bar shi ya hau zuwa mintina 30. Idan ya hau (kumbura) sai ki sami farantin gashi ki juye filawar a ciki sannan ki sanya a cikin oben ki gasa ki bar shi tsawon mintuna biyar.


Ana sai ki yanka tumatir da farar albasa da koren tattasai kanana. Sai ki koma wurin fulawarki ki duba idan ta gasu sai ki fito da ita. Sannan ki dauko kayan tumatir din da kika yanka sai ki zuzzuba akai da dan garin kayan kamshi ki barbada. Sai ki sami tsokar naman kazarki da kika yanka kanana tare ki zuzzuba akai. 

Sannan sai ki kawo mayonnaise ki yaryada akai. Sai ki zo ki rufe samansa da manshanun kanti (chease). Sanann ki mayar cikin abin gashin (oben) don ya kara gasuwa. Za ki ji yana kamshi sosai sai ki fito da shi daga ciki shi ke nan Pizza ta yi sai ci.
Tura Zuwa:

Illolin Kwalliyar Zamani Ga Fuskar Mace

Illolin Kwalliyar Zamani Ga Fuskar Mace

 

Assalamu Alaikum, Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon Shirin namu na kwalliya wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. 

Tura Zuwa:

Yadda Za Ki Hada Kazar ‘Chicken Balls’

Yadda Za Ki Hada Kazar ‘Chicken Balls’

 

Kayan Hadi


  • Kaza
  • Kwai
  • Dankalin Turawa
  • Magi da gishiri
  • Tattasai da attarugu da albasa
  • Man gyaxa
  • Kori (Curry)


Hadi

Idan uwargida ta wanke kazarta tas, sai ta tafasata da dan gishiri da albasa har sai ta yi laushi sosai, sannan a cire kasusuwan da ke jikin kazar.

A dafa dankalin Turawa ya dahu sosai sannan a ajiye ta a gefe. A markada tattasai da attarugu da albasa.

Tura Zuwa:

Muhimmacin Dabino Ga Layar Jikinmu

 

Muhimmacin Dabino Ga Layar Jikinmu

Assalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon Shirin namu na lafiya wadda yake zuwa muku kai tsaye daga shafin Duniyan Fasaha, Insha Allahu yau zamu maida dubane ga abinda ake kira da Dabino a hausance. Dabino na dauke da sinadarai na ban mamaki, sinadaran da ke da matukar muhimmanci ko dai wajen samar da waraka daga wata cuta ko kuma na hana kamuwa da wata cuta ko kuma inganta wasu sassa na jikinmu ta yadda za su gudanar da ayyukansu na yau da kullum daidai wa daida yadda kuma ya kamata.

Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *