Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Manyan Sinadaran Soyayya

Manyan Sinadaran Soyayya

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, Amin.

Ga ci gaban bayani kan ilimin soyayya don ma’aurata su fahimci wannan babban jigo na rayuwar aure kuma su dabbaka da aikatar da soyayya cikin huldodinsu da zamantakewar aurensu.

Sinadaran Soyayyar Auratayya

Ana lura da wasu muhimman abubuwa wajen fahimtar launi da ingancin soyayyar da ke tsakanin ma’aurata: wadannan abubuwa su ne kamar kayan hadin soyayya, ginshiki kuma shika-shikan soyayya.

Samun su a kammalance a cikin soyayyar auratayya shi ke sa wannan soyayya ta zama cikakkiya kuma kammalalliyar soyayya; haka kuma rashin daya ko dukkansu daga cikin dangantakar soyayya shi ke nuna nakasun wannan Soyayya.

Don haka ga bayani kan wadannan muhimman abubuwa domin ma’aurata su fahimce su, su fahimci amfaninsu da kuma yadda za su inganta su cikin rayuwar aurensu domin ya kasance dangantakar soyayyarsu ta zama kammalalliya kuma cikakkiya.

Shakuwa

Shakuwa na nufin kyakkyawar sanayya da sabo da suka kullu tsakanin mutum biyu ko sama da haka mai cike da fahimtar juna, tsananin kulawa da sadaukarwa; mutum biyun da suka shaku sosai za ka tarar kodayaushe hankali da tunaninsu a hade yake, kuma suna ajiye da kyawawan shau’uka game da juna cikin zukatansu.

Shakuwa wata aba ce mai kyau kuma mai dadi, wacce ba ta baci ko ta lalace indai har an riga an yi ta; domin in ka ji wani ya ce ‘ai mun shaku sosai da wane,’ to yana nufin sun yi zaman jin dadi, kauna da fahimtar juna.

Shakuwa nada wasu muhimman ginshikai da suke tallafarta, wadanda sai sun tabbata cikin danganta sannan ne za a iya kiran ta shakuwa, ga jerin abuwawan da ke haifar da sahihiyar shakuwa:

Tarayya

Kafin shakuwa ta kullu, sai ya kasance ana tare na wani muhimmin lokaci, kuma lokacin da ake taren nan, ana yawaita aiwatar da abubuwan rayuwar yau da kullum tare, ana yawan sabunta sanayya, ta hanyar yin ingantacciyar hira ta fahimtar juna da bayyanar da sirruka ga juna; ana fatan alheri ga juna, ana yin abubuwan faranta rai ga juna, ana taimako da kyautatawa ga juna, ana wasa da dariya da raha.

Rashin yin tarayya cikin abubuwan yau da kullum na haifar da karancin shakuwa tsakanin ma’aurata, sai ga ka ma’aurata sun dade tare har sun hayayyafa, amma ba wata sahihiyar shakuwa tsakaninsu, saboda sun ware kansu ba su yin abubuwan yau da kullum tare, kowannensu harkar gabansa kadai yake yi, ba wanda ya san abin da dan uwan aurenshi yake ciki, kila sai ibadar aure kadai suke yi tare, ko ita din suna yi ne a bukatance, ko kokarin ba da hakkin juna amma ba wata shakuwa cikinta.

Yin abubuwa tare shi ne zai haifar da babban jigon shakuwa tsakanin ma’aurata.

Sabunta sanayya

Shi ne yawan yin hira da tattaunawa game da kowane bangare na rayuwar juna, domin ta wannan hanya ce ma’aurata za su san tarihin juna, za su san komai da komia da ya faru a rayuwarsu: duka kanana da manya; masu muhimmanci da marasa muhimmaci; na farin ciki da na bakin ciki; tsoffi da suka dade da sabbi na kwana-kwanan.

Domin dan’Adam yana kara girma, hankalinsa tunaninsa da sha’ukan cikin zuciyarsa na caccanzawa, da sun canza kuma dole halayyarsa da yanayin cudanyarsa da mutane ta canza.

In ya kasance ma’aurata ba su sabunta sanayyarsu, wannan zai haifar da rashin fahimtar juna a tsakaninsu, wanda wannan wata babbar baraka ce da ke dakushe kaifin rayuwar aure ko ma ta kashe ta gaba daya.

Fahimatar Juna

Wannan shi ne babban jigo na shakuwa tsakanin ma’aurata, ya kasance sun fahimci junansu ta kowace fuska, ya kasance hankali, tunani da ra’ayoyinsu sun zamo daya a mafi yawan lokuta; sun san abubuwan so da kyamar junansu, sun fahimci yanayin halayya da sha’u’kan junansu; wannan zai taimaka musu kiyaye duk wani abu da zai kawo gardandami ko husuma tsakaninsu, kuma zai haifar musu da haduwar kai, yarda da aminta da juna.

Yarda

Wannan shi ne ya kasance ma’aurata sun aminta da junansu a yadda suke ta kowace fuska, sun fahimci karfi da raunin junansu ta kowace fuska kuma sun aminta da haka, wani abu da ya yi rauni ko ya kasa a cikin halayya ko kasantuwar dayansu bai rage daraja da kimarsa ba a idon dayansu.

Haduwar hankali da tunani

Idan ma’aurata ya kasance yanayin hankalinsu ya hadu da juna, tunaninsu game da rayuwa ya zama daya, ra’ayinsu daya game da mafi muhimman al’amura cikin rayuwarsu, sannan bukatunsu da hangen da suke ma rayuwa ya zama daya, to wannan zai sa saukake fahimtar juna tsakaninsu, kuma zai karfafa shakuwarsu.

Zan dakata a nan, sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, Amin.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *