Yadda ake girka ‘sweet and sour shrimps’
Barkanmu da warhaka Uwargida. Kamar yadda na
saba fadi cewa idan ana girka abincin Najeriya, yana da kyau a taba na wasu
kasashe ba don komai ba illa wayar da kan uwargida kan sanin nau’ukan girke
girke ko da Allah zai sa a ziyarci wadancan kasashe ba za a yi mamakin irin
girkegirkensu. Sanin girkin wadansu akwai fa’ida na ilimantar da al’umma.
Wajibi ne Uwargida ta koya wa ’ya’yanta musamman mata girki domin idan suka
kware za su iya bude wata makaranta ta koya wadannan girke girken kuma hakan
zai iya zamo musu sana’a a irin wannan yanayin da muka. shiga na rashin aiki a
kasar nan. A yau na kawo muku girkin Turawa mai suna “sweet and sour shrimps’.
Abubuwan
da za a bukata
·
‘Shrimps’
(Ana iya samunsa a manyan shagunan da ke sayar da kaji ko kifi)
·
‘Dark soy
sauce (shi ma ana iya samunsa a manyan shagunan da ke sayar da kayan abinci).
·
Sukari
·
Citta
·
Cokali
daya na garin tafarnuwa danya
·
Rabin
kofin ruwan abarba
·
Man zaitun
·
Karas
·
Attarugu
·
‘Peas’ (za
a iya samu a kasuwa inda ake sayar da su karas)
Hadi
Bayan ‘shrimps’ din ya narke sai a tsoma a
cikin ruwan ‘dark soy sauce’ sannan a saka a cikin gidan sanyi na tsawon awa
uku. Bayan haka, sai a tsame daga cikin ruwan sannan a zuba sukari da garin
citta da tafarnuwa da ruwan abarbar.
A dora tukunya a wuta sannan a rage wuta, sai
a dora tukunya wadda ba ta cika kama girki ba (nonstick) sannan a zuba man
zaitun a cikin tukunyar daga nan sai a zuba wannan ‘shrimps’ din da aka tsame a
cikin man zaitun mai zafi sai a ci gaba da juyawa. Sai a dauko yankakken karas
a zuba a ciki a ci gaba da juyawa har sai hadin ya nuna sannan a sauke a zuba a
kwano.
Wannan
irin girki ya dace da wadanda ke sha’awar rage jiki domin ba ya kara kiba.
No comments:
Post a Comment