Yadda ake shiga account wato login a blogger
Kasancewar
kana da account a blogger yakan baka damar rubuta ko saka abubuwa da dama kama
daga wanda zai amfani mutane, tallata haja kodai maka mancin hakan. Sau dayawa
mutane sukanyi korafin cewa basu san yadda zasu k’oma account dinsu ba; wasun
kuma suna cewa kamfanin google bata bada damar komawa account da aka bude ba.
Koma
dai me ka dauka ko kuma kake I’krarin cewa gaskiyar maganar anan shine yadda
zakayi login a account naka na blogger ya banbanta da yadda kake shiga account
naka na facebook da kuma twitter domin kuwa su kamfanin google suna aiki ne
bisa wani tsari domin ingan ta tsaro ta yadda ba wanda zai samu damar shiga
account naka na blogger ko kuma lalata maka ita face yana da email addreshin ka
sannan kuma yana da numbobin sirri na wannan email din.
Sabida
indai kana so ka koma account naka na blogger dole sai ka fara shiga email
addreshinka na gmail ka sanya number sirri sannan hakan zai baka damar shiga
shafinka. abinda nake so a gane anan shine wannan ba lallai bane ko wani sa’in
sai ka yinga login kafin ka shiga ba a’a shima yana da ma’adanar ajiye bayanai da
ka sanya na email addreshinka da kuma number sirrin ka face dai ka canza wayar
ko kuma ta samu matsala ka goge dukkan ma’adanar da suke ciki indai wani daga
cikin hakan ya faru ko makamancin haka to dole ne sai ka sake login da abubuwan
da ake bukata.
Cikakkiyar
hanya da za’a bi wajen shiga account na blooger
Abu
na farko da za’a fara yi anan shine ziyartar shafin gmail wato www.gmail.com tare
da sanya email addreshi da kuma number sirrin bayan an kammala haka sai a
ziyarci addreshin blogger wato www.blogger.com ko kuma www.blogspot.com
duk wanda aka sanya daga cikin biyun nan zai kai mutum izuwa waje guda ne da zarar
na’urar ya karanci wayarka ya tabbar cewa an shiga gmail account to zai kaika
izuwa shafi admin dashboard inda ake gudanar da ayyukan shafi.
Hanya
ta biyu
Idan
kuma ana so a shiga ta hanya mai sauki za’a iya ziyartar shafin blogger wato www.blogger.com
ko kuma www.blogspot.com
duk wanda mutum ya sanya daga cikin biyun nan zai kaisa izuwa waje guda ne a
can sama wajen hannunka na dama za’a ga inda aka sanya “SIGN IN” a rubuce wanda
ake nufin shiga sai a latsa kai muddin anyi hakan zai kai mutum izuwa ga shafin
gmail inda za’a bukaci email addreshinsa sai a sanya tare da latsa kan “NEXT”
daga bisani kuma zai sake tambayar number sirri sai a basa tare da latsa ma
bullin “SIGN IN” mudding an sanya abubuwan da ake bukata daidai zai mutum izuwa
ga shafin admin dashboard wato inda dai za’a gudanar da ayyukan shafin.
Sannan
duk sain da ake son a dawo dashboard na admin inda ake gudanar da ayyukann
shafin za’a je izuwa ga addreshin blogger ne wato www.blogger.com ba tare da sake bin
matakan dana gabatar ba face an goge wayar, anyi sabon waya ko kuma ana son
shiga da wata wayar shine ya zama dole a sake bin matakan.
Abun kula: Misali
ina da email addreshi guda biyu [email protected] da kuma [email protected]
sai na bude blogger da [email protected] duk sa’in da
nake so na shiga shafina na blogger dole sai na shiga da email addreshin dana
bude ba wai dan ina da guda biyu ko fiye da hakan na rudi kaina da cewar zan
iya shiga da kowannene wannan ba gaskiya bace sam dole sai da shi wancan dana
buden kawai zaiyi aiki saidai in kuma ina son na sake bude wani.
Wannan shine halaccecciyar hanya da
ake bi wajen shiga account na blogger ku kasance tare da Duniyar Fasaha domin
samun ingatacciyar dabaru daga bangare daban daban; naku a koda yaushe Jikan
marubuta kuma sharifin zamani ‘Muhammad Abba Gana’.
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:
Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan