Jirgin
masoyane
Tare
da
Muhammad
Abba Gana
So
yakan zamo tamkar tsiro a cikin zuciya, yayin da a gefe guda kuma yakan zamo ♥❤
So tamkar mayafin rufe ne, shi yasa ma wasu kan yi wa
so lak’abi da suna marurun zuciya.
Bege shine mutum koda
yaushe ya dinga tunanin wanda ransa ke so, ba wai ana nufin ya zauna koda
yaushe bashi da aiki sai tunani ba. Abinda ake nufi shine, babu dai yadda
za’ayi a dau lokaci ba a yi tunanin masoyiya ko masoyi ba.
Kuma akwai wasu misalai da
dama wadanda suke nuna mutum yana bege, ko ya shiga cikin begen masoyinsa.
Wadannan abubuwa kuma idan
mai karatu yayi Nazari akan su, zai tabbatar da hakanne, kamar yadda kila ta
taba faruwa a kanshi.
Da yawa wasu kan shiga
cikin soyayya su kuma samu kansu a yanayin zazzafan begen so, wanda ke haifar
da yawan tunanin wanda ake so din.
Kuma a irin wannan
yanayin, mutum kan shiga cikin wata yar damuwa ya zamo tamkar mara lafiya, ko
wani maraya wanda yayi rashin iyaye, ko makamanciyar haka.
To a kowanne irin hali dai
mutum samu kansa a cikin yanayin bege, ana so ya dinga jurewa saboda so shu’umi
ne.
No comments:
Post a Comment