Basir
yana samuwa ne a lokacin da jijiyoyin da ke mafitar bahaya suka kumbura daga ciki ko daga waje (wanda
muke kira basir mai tsiro), wanda yawancin lokuta hakan na faruwa ne a
sakamakon wahala wajen fitar
da bahaya. Basir yafi matsawa wadanda ke da matsalar jinkiri wajen narkewar
abinci a ciki, masu ciki da kuma tsofafi.
Duk
da dai wannan matsala ba ta haifar da wata barazana ga rayuwar mutum, rashin
dadin da take haifarwa ya kan matsawa mutane sosai har su ta shan magunguna
barkatai, wanda akarshe ba lallai bane hakan ya zama alkhairi a garesu. Mujallar
Duniyan Fasaha ta kawo muku hanyoyin magance wannan matsala guda biyar masu
matukar sauki wadanda suka kunshi abubuwan da muke amfani da su na yau da
kullum.
1.==> Man zaitun
Man
zaitun ba’a barshi a baya ba wajen magance basir domin kuwa yana taimakawa
matuka wajen kara laushi da kuma taushin jijiyoyin da ke hanyar fitar da bahaya wanda hakan
na rage wahalar da ake sha matuka. Ana shan cokali daya ko biyu na man zaitun
tare da abinci a kowace rana domin ganin alfanunsa.
2.==> Man Kwa-Kwa
Ana
shafa man kwakwan ne a gurin kumburin akai akai idan basir din na waje ne,
banda ragen radadin ciwon da hakan yake yi, za’a ga girman shi ya fara raguwa a
cikin ‘yan kwanaki.
3.==>
Aloe Vera
Aloe
vera yana taimakawa wajen kawar da radadin basir a cikin lokaci kalilan. Ana
amfani da shi ta hanyoyi guda biyu: ko dai a matsa ruwan a shafa a gurin
kumburin ko kuma a yayyanka ganyen a fere kayoyin sanna a sanya shi a firiji ya daskare, sai ana
dorawa akan kumburin. Hakan yana taimakawa matuka wajen motsar da kumburi.
4.==>
Leman Tsami
Shima
leman tsami ana amfani da shi ta hanyoyi guda biyu. Ana hada ruwan shi da citta
da kuma zuma a na sha, sannan kuma ana shafa ruwan leman tsamin a waje. Hakan
yana magance kumburin da ya ke daga ciki da kuma wanda yake daga waje, ya kuma
magance radadi.
5.==>
Kankara
Ana
fasa kankara a kunshe ta a cikin tsumma mai tsafta, sannan ana dannawa akan
kumburin. Hakan yana kawo saukin ciwon sosai kuma ya rage kumburi.