Yadda ake cincin mai kama da kek
Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan lokaci
uwargida, tare da fatan an yini lafiya. Mata da dama ba su iya amfani da fulawa
wajen sarrafa ta wajen yin kayan marmari ba. Da yawan mata sun fi kwarewa ne a
harkar girke-girken da ake yin su da albasa da kayan miya. Ganin hakan ne yasa
a yau na kawo muku yadda ake yin cincin mai kama da kek. Tare da fatan za a
gwada a gida domin sanya kunnuwan maigida su yi motsi. A sha karatu lafiya.
1.
Fulawa
2.
Suga
3.
‘Baking
powder’
4.
Butter/
man gyada
5.
kwai 15
Da farko dai, za a samu kwano ko roba sannan
a fasa kwai guda goma sha biyar a ciki. Bayan haka sai a samu kofi tsaka-tsaki
a auno suga daidai girman wannan kofi sannan a zuba a cikin ruwan kwan a yi ta
gaurayawa har sai ta narke. A sake dauko wannan kofin da aka auna suga a narkar
da ‘butter’ sannan a zuba a kofin har sai ya cika sannan a zuba a cikin hadin
suga da kwai a cigaba da motsawa da muciya, sannan a debo ‘baking powder’
babban cokalin cin abinci daya ya cika sosai sannan a zuba. A cigaba da
gaurayawa. A sake debo fulawa daidai cikin wannan kofin da aka auno suga da
sauransu a auno fulawa kofi daya sannan a zuba a cikin hadin a cigaba da juyawa.
Idan hadin ya yi ruwa-ruwa sai a dan kara fulawa kadan ta yadda in an sanya
hannu ba zai manne ba. Amma kada a bar fulawar ta yi taurin hadin cincin din da
aka saba.
A wanke hannu a goge sannan a gutsuro wannan
kwabin a danna a tafin hannu a mulmula sannan a yi masa rami a tsakiya kamar
awarwaron da yara mata ke sanya wa a hannu, sannan a dora man gyada a kan wuta
a soya. A bar shi a kan wuta domin hadin ya soyu daga nan sai a soke. Za a iya
cin irin wannan cincin da shayi da kuma lokacin da za a tarbi baki.
No comments:
Post a Comment