Muhimmancin Ilimin Computer – Kowa ya iya
allonshi ya wanke
Ko ba a gwada ba an san linzami yafi karfin
bakin kaza, domin mahimmancin computer da iliminta ya wuce a ce mutum bai sani
ba. Domin ko ba a fada maka ba lura da yadda ta mamaye kusan mafi yawanci abubuwan
mu na yau da kullun. tun daga makarantunmu, ma’aikatunmu kasuwancinmu, asbitocinmu,
gidajen yada labarai da makamantansu, dukkanin su za ka samu a na amfani da ita
Computer.
Kusan a wannan zamani, computer ta samar da
sauki wajen tafiyar da alamura ga dan adam. Kama daga rubutun takardar wasika
zuwa takardar sanarwa ta wajen aiki ko takardar notice, takardar biyan albashi
da lissafin kudaden kasa dayin kasafin kudi, hada da harkar hada- hada, da
bayanai na kididdiga da fitar da kudade a bankuna, duk computer ta kawo sauki
ta kowanne fanni.
Haka kuma computer ta samar da sauki wajen
tafiyar da harkar banki, ka duba ATM yanda yake, computer take karbar cheque ko
kuma ta baka kudi, ko kuma ta cireshi. Ga wadanda suke sayan kaya a kasashen
waje suna amfani da computer wajen duba yanayin kayan su da kuma sannin a wane
wuri kayan suke da kuma lokacin da kayan zasu iso. Ta bangaren kasuwanci, idan
ka zuba wa computer bayanan harkar kasuwancin ka, kayan daka siyo, ka ware mata
kudaden wahalhalunka, kama daga kudin abinci, kudin sallamar ma’aikata, kudin
dauko kaya, kudin shago da kudin wuta za ta fitar maka da ribarka ko kuma
faduwarka a dan kankanin lokaci.
Haka za ta iya a jiye maka wasu mahimman
bayannanka bayan tsawo shekaru idan ka nemi ta fitar maka za ta fito maka da
su. Haka da zamu koma wajen fanin kula da lafiya ana amfani da computer wajen
binciko yanayin cuta da mazauninta a jikin dan adam, ba tare da likita ya
tambaye shi ba, hakanan ana iya bincikar cikin da mace take dauke da shi a gane
lafiyar shi ko rashin lafiyar shi da yanayin kwanciyar shi, duk a cikin dan
kankanin lokaci. Dawo bangaren makarantu zaka samu suna amfani da computer
wajen saukaka bincike da nazarin darussa ga yara. Sukan yi amfani da ita
computer ta wajen kimiyya da fasaha don gano adadi da kididdiga. Ana samun
na’ura da take dauke da muhimman takardu ga daliban fiye da dubu dari uku wanda
zai yi wahala a sami wani laburari a karamar makaranta dake de littafi daban
daban har dubu goma.
Ta hanyoyin sadarwa computer tana taimakawa
gidajen jarida, da na watsa labarai wajen gyare gyaren tarin rubutu, video da
sauti wanda a dan kankanin lokaci sai su gyara ayyukansu don watsawa don haka
da taimakon computer ba sa bukatar sai sun shiga studio kafin su dauki bayanan da
za su watsa. Haka nan sadarwa da aka samu ta yin amfani da wayoyin ta fi da
gidanka(salula) za ka iya rabuta wasika ka aika, zaka iya aje alama ta
tunatarwa, zaka iya daukar hoto ko video zaka iya yin lissafi da dai
makamatansu ciki dan kankanin lokaci ba tare da wahala ba. Kasancewar ci gaban
internet ya mamaye dukkan fannonin rayuwar dan adam a yau ba ta tafiya yadda ya
kamata sai da internet ilimin computer shine sinadarin cin moriyar internet Idan
kuwa muka duba bangaren tsaro, a zamanin da, zaka samu yana da wahala a gano
file (kundin) na laifi da mutum yayi bayan an kai shi kotu, amma yanzu da zarar
an saka bayanan shi, nan take za a samu, ka duba irin Computer da take bincikan
‘yan yatsu da fuskar wanda ake zargin shi da laifi, ko da yake yanzu ne aka
fara irin wannan tsari a wannan kasa ta mu Najeriya.
Haka idan ka duba hatta cikin motoci da
abubuwan hawa kamar jirgin sama, da jirgin kasa da jirgin ruwa za ka samu akwai
computer a jikinsu, daga abinda yake sarrafa yanayin zafi ko sanyin abin hawa
computer dake ciki take tafiyar da shi. Ballantana uwa uba ire-iren abubuwan
hawa da ake kerowa na zamani a yanzu akwai motar da ake samun computer a cikin
ta wacce duk inda wannan motar take a duniya za a iya kashe ta ko kuma a kunna
ta, haka nan jirgin sama muna da labarin jirage irin na yaki wanda kasahen da
suka ci gaba suke da su wadanda babu matuki a cikinsu, computer da ke ciki ita
take sarrafa su, wanda ko da abokanen gaba sun harbo wannan jirgin to ba za a
rasa rai ba. Computer ta kawo sauki ga masu ayyuka irin wanda a da sai an dauki
tsawon lokaci ko kwanaki kafin ace an kammala su. Misali abin da ya shafi
lissafin dukiya don fitar da gado an sami sauki mai yawa ,idan ka duba Computer
da take rabon gado wanda duk abinda mutum ya mallaka komai yawansu, komai yawan
wanda za su gaje shi, da zarar an gama zuba mata bayanan dukiyar da magadan
sakon biyar yayi yawa ta gama raba wannan gado kamar yadda Allah madaukakin
sarki ya fadi ayi ba tare da ta rage wani abu ko ta karashi ga wani ba. Mu koma
bangaren kere-kere shima Computer tana taka mahimmiyar rawa wajen kere- keren abubuwa
wanda a zamanin da, sai an sami karti majiya karfi suke iya kera wannan abun.
Idan muka koma harkar zane zane, yanzu an kai fagen da idan ka nuna fili kace
ga girmanshi, kana son bishiya kaza, filawa kaza, kana kuma son mota irin kaza,
ga irin fenti da kake so, ga irin kofofi da dai dukkan abinda za ka fadi da ya
kamata a ganshi, kana gama lissafi wanda zai zana maka gidan yana kwafewa a
‘yar karamar takarda a hannunshi, da zarar ya gama zana gidan sai yayi amfani
da daya daga cikin program na Computer ta gina wannan gida a cikin ta kamar
yadda kace kana son, ka ganshi kamar da gaske babu wani abu da za ka ce ba na
gaske bane, wanda idan kace kana son a bude maka cikin gidan kaga yadda kujeru
da bayi da kayan kichin suke duka za ka gani. Kuma idan aka gama gina maka
gidan na zahiri za ka ga babu bambanci tsakanin na cikin Computer da naka na waje.
Everyone loves it when people come together and share opinions.
ReplyDeleteGreat site, continue the good work!