Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi

Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi

Yadda za’a magance matsalolin fata a sanyi


A halin yanzu, sanyi ya fara sallama a wajaje da dama. Da zarar an fara ganin hazo ko hunturo lallai wannan alama ce ta nuna cewa sanyi ya shigo. A wannan lokutan ne yakamata a fara takatsantsan wajen kulawa da fatar jiki. Idan ba’a kula da fatar ba, har sai da ta gama bushewa ko yin gautsi, hakan na daukan lokaci kafin a samu a magancesu. Don haka ne a yau na kawo muku yadda za’a magance matsalolin fata a lokacin sanyi.

1.==> Man kadanya: tun yanzu ne yakamata a fara amfani da man kadanya a fata. Yin hakan kamar rigakafi ne domin magance matsalolin fata. Idan fata ta fara datsewa sakamakon sanyi, dole ne a yawaita shafawa domin man kadanya na dauke da sinadarai masu warkar da cututtukan fata.

2.==> Kaushin fata: idan an kasance ana da kaushin fata, dole ne a dunga sanya man ‘glycerin’ a cikin man shafawa. Koda alwala akayi yana da kyau a yawanta shafa man domin samun saukin lamarin.

3.==> Fason kafa: yana da kyau a rika sanya takalma masu laushi ba masu tauri sosai wadanda zasu rika illata fatar ba. Idan an kasance ana da fason kafa, sai a rika tsoma kafar a ruwan dumi da gishiri na mintuna goma sannan a rika gogewa da dutsen goge kafa sannan a shafa man ‘glycerin’ sannan a sanya safa kafin a kwanta a kullum domin samun saukin matsalar.

4.==> Sulbin fatar fuska; a samu ayaba sannan a kwaba ta tare da kindirmo sannan a rika shafawa a fatar fuska a bari na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi a bari fuskar ta bushe da kanta kafin a shafa mata man fuska.


5.==> Karyewar gashi: kada a rabu da man zaitun a koda yaushe. A kasance ana sanya shi a gashi da zarar anji fatar kai ta fara bushewa. Yawaitar sanya man zaitun ko kuma man kwakwa na hana gashin kai zubewa.
Tura Zuwa:

Kula da gashin kai a hunturu

Kula da gashin kai a hunturu

Assalamu Alaikum matan gidan nan tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Na dan tafi hutu ne amma da yardarr Allah na dawo lafiya. A yau na kawo muku yadda za a kula da gashin kai a lokacin hunturu. Gashin kawunanmu na bukatar kulawa sosai saboda gashin ‘ya mace na cikin abin da yake kara mata kyau. Akwai abubuwa da dama wadda ya kamata ki yi amfani da su kamaru; man zaitun, zuma, man ‘castor’, ruwan lemun tsami, man kwakwa. Wadannan nau’ukan mai na da inganci sosai musamman ma wajen kare gashi daga tsinkewa da kuma sa shi karfi, santsi da sheki.

Man kasto: Man kastor (castor oil) na taimakawa wajen gyaran gashin kai a hunturu. A debo man kastor kamar cokali uku. Sai ki shafa a fatar kai sanan sai a taje a hankali. A tirara tawul har sai ya yi zafi. Sannan a daura tawul din mai zafi a kai na tsawon minti goma sha biyar. Bayan haka, sai ayi wanka. Yana hana gashi tsinkewa da hunturu.

Man zaitun da zuma: A hada cokali uku na man zaitun da cokali daya na zuma. A kwaba hadin har sai ya gaurayu sosai, sannan a shafa hadin a kan fatar kai. Bayan mintuna kadan, sai a wanke da ruwa da sabulun wanke gashi. Kwai, ‘binegar’ da man kwakwa A kada kwai daya, sai a sa man kwakwa cokali biyu da binegar. A hadin nan hadin waje daya. Sai a kwaba su. A sa hadin a fatar kai sannan sai a taje gashin kai. A bar hadin ya jima tsawon minti goma sha biyar. Sai a wanke da ruwan dumi.

Lemun tsami da man kwakwa: A hada cokali biyu na man kwakwa, cokali daya na ruwan lemun tsami. Sai a gauraya hadin har sai ya gaurayu sosai. Sannan a shafa a kan fatar kai. Wannan hadin na warkar da amosarin kai, da kuma hana gashi tsinkewa.

Man zaitun: Man zaitun na da matukar inganci musamman ma ga gashi mai gautsi. Fatar kai na saurin bushewa saboda hunturu. Idan ana da irin wannan kai, sai a dumama man zaitun a tukunya idan ya yi zafi, sai a shafa a fatar kai. A ci gaba da murza man a fatar kai har sai man ya shiga fatar sosai. Sanan sai barshi kamar tsawon minti goma sha biyar. Bayan haka sai a wanke.
Tura Zuwa:

Yadda Ake Chanza kallar rubutu a shafin blogger

Yadda Ake Chanza kallar rubutu a shafin blogger

A wasu sa’in mutum yakan so chanza kallar rubutunsa don ado ko kuma dan banbanta kalma tsakaninsa da suran. Ko ma dai me manufar mutum yake insha Allahu a wannan makon zamu tattauna ne game da yadda ake canza kallar rubutu a blogger wato wajen rubutun shafi a yanar gizo.

            A hakikanin gaskiya chanza kallar rubutu a shafin blogger ba wani abune mai matukar wahala ba ko kuwa yana bukatar wasu matakai masu tsauri ba. A’a sam bai da wani wahala face duk sa’in da mutum yake son canza kalar rubutu sai ya bi yan wasu matakai masu saukin gaske.

Matakai da ake bi wajen canza kallar rubutu a shafin Blogger  

1.==> Da fari mutum zai ziyarci wajen da ake posting ma’ana wajen da ake saka abunda aka rubuta wanda mukayi bayani dalla dalla a makon daya gabata Yadda ake sa rubutu (post) a Blogger cikin sauki.

2.==> Yayin da mutum ya kammala rubuta abunda yake son sawa sai ya zabi kalaman dayake son chanza wa kallar ta hanyar yin highlighting nasu sannan ya danna mabullin Kalmar 'A' wadda yake dan sama ta bangaren hannunsa na dama sannan mutum ya zabi kallar da yake so.

Yadda Ake Chanza kallar rubutu a shafin blogger


Za’a iya bin wannan matakan koda kuwa an sa kallar ana kuma son sauyawa.

Wannan shine takaitacciyar hanya da ake bi wajen chanza kalar rubutu a shafin blogger dafatan wannan ya taimaka matuka, a kasance tare da shafin Duniyan Fasaha dan samun sabin abubuwa da zasu amfaneku a yau da kullum. Naku a yau da kullum Jikan Marubuta Muhammad Abba Gana. Bissalam!! 

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Yadda ake jus din gurji mai zobo

Yadda ake jus din gurji mai zobo

Yadda ake jus din gurji mai zobo


Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na girke girke wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha tare da fata ana cikin koshin lafiya. Yana da kyau a san yadda ake yin nau’ukan girke girke da kuma mahadinsu. Ina nufin jus ke nan. Duk dadin abinci yana bukatar mahadi da zai dada wa girkin armashi. Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake wata mahadar girki; jus din gurji.

Abubuwan da ake bukata

·              Gurji
·              Kankana
·              Ayaba
·              Lemu
·              Amfuna
·              Gwanda
·              Zobo
·              Flaba
·              Sakari
·              Citta
·              Kanumfari

Hadi

A sami gurji kamar goma sai a fere sannan a markadasu a na’urar markade a tatse ruwan a ajiye a gefe. A sami kankana a yayyanka kanana sosai a wata roba da ayaba da amfuna da gwanda duka a yayyankasu kanana sannan a ajiye a gefe.

A tafasa zobo da kayan kamshi kamar su citta da kanamfari da kuma bawon abarba. Sannan a tafasa sosai sannan a tace a ajiye ya huce sannan a zuba sukari da flaba sannan a sanya a gidan sanyi.


Bayan haka, a debo wannan ruwan gurjin a zuba a zobon sannan a zuba wadannan yankakken ’ya’yan itatuwan a zubasu a kofi sannan a zuba wannan jus din zobon. Ana sha ana tauna.
Tura Zuwa:

Yadda ake masa

Yadda ake masa

Yadda ake masa


Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama wadanda ake bi don yin masa. Yadda wata zata tsara na ta masar daban take da yadda wata uwargidan za ta sarrafa na ta. Akwai nau’ukan masa da dama kamar masar Gero da Dawa da Semo da kuma Shinkafa da dai makamantansu. A yau na kawo muku yadda ake masar Shinkafa a cikin hanya mai sauki ba tare da an bada ayi ko kuma a saya ba.

Ababen da ake bukata

·              Danyen shinkafa
·              Albasa
·              Man gyada
·              Yis da ‘baking powder’
·              Siga
·              Albasa

Hadi
A jika danyar shinkafa na tsawon awa daya sannan a wanke ta carak a zuba a cikin na’uran markade. Sannan a tafasa shinkafar kadan kafin ta nuna sosai sai a sauke a zuba a cikin wannan danyar shinkafar sannan a yayyanka albasa a kai sannan a markada har sai shinkafar ta yi laushi sosai sannan a zuba a cikin roba.

Bayan haka, sai a zuba yis a ruwan dumi kadan sannan a zuba a ciki. A sake dauko ‘baking powder’ a zuba a gauraya sosai sannan a rufe a sanya a rana har sai hadin ya tashi.

Sannan a dauko Tanda a daura a kan wuta. A zuba siga a roba da ruwa kadan yadda za ta narke sannan a zuba a kullun masar a sake gaurayawa . sannan a zuba man gyada kadan idan ya yi zafi sannan a debo kullun a zuba a ramukan tandar. Idan ya dan nuna sannan a sake juya masar zuwa dayan gefen domin ta nuna. Bayan ta nuna sannan a sauke a sanya a kwano.



Za a iya cin wannan masar ko waina da yajin kuli ko miyar taushe ko kuma miyar Alayyahu. A ci dadi lafiya.
Tura Zuwa:

Cin Kayan Lambu Na Bayar Da Kariya Daga Cutar ‘Endometriosis’ Mai Hana Haihuwa

Cin Kayan Lambu Na Bayar Da Kariya Daga Cutar ‘Endometriosis’ Mai Hana Haihuwa 

Wani likita a fannin cututtukan mata a Nijeriya dakta Adewole Akintoyose ya yi kira ga mata da su jimirci cin kayayyakin itatuwa da na lambu domin kare kansu daga wata cuta mai hana haihuwa mai suna “endometriosis” a turance.

Adewole, wanda ma’aikaci ne a asibitin St Leo da ke unguwar Lekki a jahar Lagos ya ce wannan cuta ta fi yawaita a tsakanin mata ‘yan shekaru 25 zuwa 40.

A fadarsa, Cutar na yin lahani ne ga mahaifa da kuma kwayayen da ke jikin mace. Likitan ya ce alamomin cuta sun hada yawan ciwon mara, zafi a yayin saduwa, yawan gajiya, zafi yayin fitsari, da sauran su.

Sauran alamomin sun hada da rashin haihuwa da wuri, fara gani jinin haila da wuri, da daina haihuwa a lokacin da ya kamata.


Ya gargadi mata da su rage cin naman shanu, wanda ya ce ka iya haifar da cutar, ya kuma shawarci su da su kara yawan kayan itatuwa da na lambun da suke ci, wanda hakan na matukar taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da cutar.
Tura Zuwa:

Muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwa

Muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwa

Muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwa


Assalamu Alaikum! Ina yi mana gaisuwa wadda ta dace da al’umma. Allah Ya kara mana ni’imar rayuwa da zaman lafiya a kowane lokaci, Amin.

A wannan makon kuma, za mu duba muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwar dan Adam. Har kullum riba da nasara na nan ga mutumin da ya yi aiki tukuru a rayuwarsa. Domin kuwa komai ka gani a rayuwar nan, yana da sanadin faruwarsa, kamar kuma yadda babu yadda za a yi ka kama zomo ba tare da ka ci gudu ba. Duk wani abu mai kima da muhimmanci, ba a samunsa a haka nan, watau a bagas, kamar yadda masu iya magana kan ce.

Aiki tukuru ba yana nufin ka dawwama, tun daga fitowar rana zuwa faduwarta kan abu guda ba, a’a, ba haka ake nufi ba. Duk aikin da za ka yi, ka tabbatar ka ba shi isasshen lokacin da ya dace, kuma ka aiwatar da shi da gaske ba tare da kasala ba. Sannan ka tabbatar ka ware lokacin sararawa da lokacin cin abinci da lokacin yin ibada, sannan kuma da lokacin tashi daga aikin nan naka. Aiki tukuru na nufin ka yi adalci tsakaninka da aikin kansa da kuma yin adalci ga kai kanka da jikinka, sannan kuma ka yi wa wanda ya sanya ka aikin adalci. Da ikon Allah, za ka samu biyan bukata daidai gwargwado.

Gaskiya da rikon amana, abin dubawa ne wajen gudanar da aikinka ko sana’arka. Su ma wadannan sinadarai ne na sirrin samun nasarar aiki ko sana’a. Sai dai dole mutum sai ya dode kunnuwansa daga surutan mutane, domin a wannan zamani, duk wanda ya ce zai mayar da hankali kacokan ga aikinsa bisa gaskiya da adalci, zai zama wani bako a wurin aikin nasa, domin za a rika kiransa da wasu sunaye na shagube. Za ka ji ana cewa ‘ina ruwan agogo sarkin aiki!’ Ko kuma a rika ce masa ‘Gadu mai aikin banza!’ Ko kuma saboda tsare ka’idar lokaci da ba komai da kowa hakkinsa, sai ka ji ana ce masa ‘wane bai waye ba.’

Irin wadannan maganganu, kada ka yarda su karya maka gwiwa, kada ka amince su maido da kai baya. Duk abin da za ka yi, ka tabbatar kana da yakinin yinsa a zuciyarka, ka tabbatar bisa dokar aiki yake. Idan ka yi haka, komai daren dadewa, kai ne kan nasara, kuma za ka gane amfanin tsare aikin naka, za ka ga ranarsa, wata rana. Domin kuwa duk abin da ka bauta masa, sai ka ci gajiyarsa. Duk abin da ka sadaukar da lokacinka da karfinka da tunaninka wajen aiwatar da shi, to babu shakka ba zai fadi kasa a banza ba. Za ka samu sakamakonsa, komai tsawon lokaci.

Wannan al’amari, kamar yadda misalai suka gabata, mujarrabi ne. Idan ba ka amince ba sosai, tsaya tsaf da ranka ka natsu. Dubi tarihin wani magabaci da kake ganin ya ci nasarar rayuwa, ko kuma ya kai kololuwar nasarar aikinsa ko kasuwancisa. Yi masa tambaya cikin kwanciyar rai, ka ji irin surkukin dajin wahalar da ya ratsa kafin ya kai ga wannan matsayi. Na tabbata idan dai ya ba ka labarinsa tiryan-tiryan, za ka iske cewa ba haka nan ya samu nasarar ba. Ba yana zaune haka siddan aka ba shi nasarar ba. Don haka, raggo dai ba ya suna, kuma duk wanda bai tsaga ba, ba zai ga jini ba, wanda duk bai gina rijiya ba, ba zai samu ruwa ba.

Don haka, kai dai maida hankali ga aikinka, komai kankantarsa, komai rashin ingancinsa, ka yi amanna, sannan ka ci gabadaaiwatar da shi. Babban burinka da farin cikinka na nan tafe wata rana. Babu mamaki ba za ka zama gagarabadau ba a fagen naka, amma dai za ka iya kawo canji na alheri ta wanan aiki naka. Watakila ba za ka iya zama farin wata gama duniya ba, amma kana iya zama wata karamar tauraruwa mai haska ma wasu hanya, a rayuwarsu. Domin a rayuwar nan tamu, ba a taru aka zama daya ba. Zama ne na ’yan marina, kowa da inda ya sanya gabansa.


Babban darasinmu na yau shi ne, kada mu karaya, mu jajirce mu yi aiki tukuru, bisa amana da adalci da gaskiya. Allah Ya taimaka mana, amin. Sai kuma mako na gaba idan Allah Ya kai mu. Wassalam!
Tura Zuwa:

Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki

Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki


Email yakan bamu damar tura abubuwa da dama kama daga rubutaccen sako, sauti, hoto da kuma hoto mai mosti cikin sauki zuwaga abokan hulda ko kuma abokan arziki. A makon daya gabata nayi cikakkiyar bayani dalla dalla ma’anar sa da kuma yadda ake bude shi tare dashi gmail. A wannan karon kuma insha Allahu zan nuna muku hanyar da ake bi wajen shiga account na gmail din da aka bude.

Matakin Farko: Mutum zai ziyarchi addreshin gmail din wato www.gmail.com zai kaisa izuwa ga shafin nan wanda shine babban shafinsu na shi gmail.
A sama can bangaren hannun dama mutum zaiga inda aka rubuta “Sign in” wanda ma’anar sa a hausance shiga ciki. ba lallai bane mutum yaga wannan shafin mafi yawancin lokutan yana kai mutum ne izuwa ga mataki na biyu koda yake ya dan ganane da wani irin browser mutum yake aiki dashi ko kuma wani irin salula mutum ke aiki dashi a mafi akasarin lokutan yana nunawane wa masu aiki da chrome browser ko kuma masu aiki da kwanfuta.

Mataki na Biyu:  za’a umurci mutum yasaka email nasa a dan akwatin dake k’asan nan misali email namu na shafin nan shine [email protected] sai na sanya shi a cikin akwatin tare da latsa ma bullin “Next” 

Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki


wanda zai bada damar zuwa mataki nagaba. Akwai wasu sa’in da zai rubuta wa mutum “Email not found” kodai maka mancin haka yana gayawa mutum cewar email daya sanyan nan ba dai dai bane wata kila an yi tuntuben kalma wajen rubutu dole mutum ya lura a lokacin da yake rubutawa dan gujewa kuskure.  

Mataki na Uku: Zai tambayi mutum ya sanya numbobin sirri wato wanda aka fi sani da password a turance, sai mutum ya sanya shi tare da latsa mabullin “Next” 
Yadda ake shiga Email wato na Gmail cikin Sauki

in dai mutum ya sanya numbobin sirrinsa daidai zai kaisa izuwa ga account nasa in kuma ba dai dai bane zai fito da wani rubuta mai kala ja dauke da “incorrect password” ko kuma “wrong password” koma wanne ya sanya maka daga ciki yana gaya maka cewar numbobin sirrin ba daidai bane sai ka goge su sannan ka canza zuwa wani wanda ka sanya a lokacin da kake budewa.


Wannan shine cikkakiyar hanya da ake bi wajen shigan email naka na gmail ku kasance tare da Duniyan Fasaha don samun sabbin ababe da zasu amfaneku a al’amuran yau da kullum.      

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Yadda za a magance kodewar fata

Yadda za a magance kodewar fata

Kodewar fata na aukuwa ne a lokacin da mutum ya kasance yana yawan shiga cikin rana domin neman halaliyarsa ko kuma don yini a rana. Idan hakan ta kasance, sai fatar ta zama baka. Wannan abu ya fi aukuwa ne a fuska. Sai a ga fuskar gefe daya ta yi baki daya gefen kuma da dan haske. Wannan abu ba a sanin lokacin da suke faruwa. Shi ya sa a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi don neman kariya daga wadannan kunar ranar ko kuma kodewar fata.

Ruwan dankalin turawa; a fere dankalin turawa sannan a wanke sai a kankare a matse ruwan sannan a rika shafawa a fuska musamman inda fatar ta kode. Yin haka na magance matsalar fatar sannan kuma yana kare sake aukuwar hakan.

Madara; a samu madara a sanya a gidan sanyi har sai ta yi sanyi sosai sannan a samu tawul karami a rika tsomawa ana goge fuskar da shi. Madara na sanya hasken fata sannan kuma tana warkar da wannan kodewar fatar.

Ruwa; a yawaita shan ruwa sosai idan ana dauke da wannan matsalar sannan za a iya sanya ruwan ya yi kankara sannan a rika shafa wannan kankarar a inda fatar ta kode.

Gurji; a samu gurji sannan a yanka sannan a sanya a gidan sanyi har sai ya yi kankara sannan a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode ko kuma a rika daurawa wurin har sai ya narke.

Koren ganyen shayi; za a iya tafasa koren ganyen shayi hade da na’ana. Bayan sun tafasa sannan a bari hadin ya jiku kamar na tsawon sa’a daya sannan a sanya a gidan sanyi, sannan a wanke fuskar da hadin ko kuma a samu auduga ana shafawa a inda fatar fuskar ta kode.

Ganyen ‘aloe bera’; a samu wannan ganyen sannan a matse ruwan da ke ciki a rika shafawa a fuskar a kullum har sai kodewar ta yi sauki. Wannan ganye na da matukar mahimmanci a fatar mu don haka yana da kyau a kowane gida a shuka.

Ruwan tuffa; za a iya samun wannan ruwan ne bayan an kankare sannan a matse. Sai a rika shafawa a fuska har sai ya bushe. Haka za a rika yi a kullum.


Masu karatu kada su hada duka wannan hadin su ce za su yi shi a lokaci guda. Sai dai su zabi daya daga cikinsu. Hada wadannan ababen da na lissafo na iya haifar da wata cutar fatar fuska. Da fatan za a kiyaye.
Tura Zuwa:

Tuwo miyar kuka

Tuwo miyar kuka

Assalamu Alaikum Uwargida tare da fatan alheri. A yau na kawo muku yadda ake tuwo miyar kuka. Lallai wannan irin girki ne wadda yara da dama basu cika so ba. Kasancewar yadda wadansu mata ke girkawa. Ko kun san cewa wannan miyar ba ta karamin gida bace idan har an san yadda za a sarrafa ta?
Wannan miya ce ba na hana yaro kuka ba, har ma da manya. Domin babu abin da ya kai ta sauki wajen hada ta musamman idan aka hada da tuwon masara ko dawa. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da za a bukata

·           Kuka
·           Tafarnuwa
·           Banddar kifi
·           Kaza/nama
·           Citta
·           Attarugu
·           Albasa
·           Magi
·           Kori
·           Man shanu
·           Daddawa

Hadi

Da farko Uwar gida za ta wanke kazarta ko nama yadda ya kamata sannan ta daura a wuta. Ta yayyanka albasa da tafarnuwa da dan gishiri kadan sosai, har hadin ya tafasa. Sannan ta dauko kifi banda kamar daya ta wanke da ruwan zafi sannan ta zuba. Ta jajjaga attarugu hade da tafarnuwa da daddawa sai sunyi laushi sannan ta zuba. Ta samu garin citta kadan ta zuba da magi da kuma kori.

Idan an fara jin kamshin kifi ya bayyana, alama ce cewa kifin ya nuna sannan a tsame kazar ko namar a ajiye a gefe sannan a debo garin kuka a rika kadawa kadan-kadan ta yadda ba za ta yi gudaji ba. Sannan ta rage wuta ya dan sake tafasa kadan. Idan tana bukatar sanya tokar miya, sai ta zuba kadan ta sake gaurayawa sannan ta sauke.

A tuka tuwon dawa ko na masara ko kuma na shinkafa sannan aci da man shanu.
Tura Zuwa:

Yadda ake shiga account wato login a blogger

Yadda ake shiga account wato login a blogger

Yadda ake shiga account wato login a blogger


Kasancewar kana da account a blogger yakan baka damar rubuta ko saka abubuwa da dama kama daga wanda zai amfani mutane, tallata haja kodai maka mancin hakan. Sau dayawa mutane sukanyi korafin cewa basu san yadda zasu k’oma account dinsu ba; wasun kuma suna cewa kamfanin google bata bada damar komawa account da aka bude ba.

Koma dai me ka dauka ko kuma kake I’krarin cewa gaskiyar maganar anan shine yadda zakayi login a account naka na blogger ya banbanta da yadda kake shiga account naka na facebook da kuma twitter domin kuwa su kamfanin google suna aiki ne bisa wani tsari domin ingan ta tsaro ta yadda ba wanda zai samu damar shiga account naka na blogger ko kuma lalata maka ita face yana da email addreshin ka sannan kuma yana da numbobin sirri na wannan email din.

Sabida indai kana so ka koma account naka na blogger dole sai ka fara shiga email addreshinka na gmail ka sanya number sirri sannan hakan zai baka damar shiga shafinka. abinda nake so a gane anan shine wannan ba lallai bane ko wani sa’in sai ka yinga login kafin ka shiga ba a’a shima yana da ma’adanar ajiye bayanai da ka sanya na email addreshinka da kuma number sirrin ka face dai ka canza wayar ko kuma ta samu matsala ka goge dukkan ma’adanar da suke ciki indai wani daga cikin hakan ya faru ko makamancin haka to dole ne sai ka sake login da abubuwan da ake bukata.   

Cikakkiyar hanya da za’a bi wajen shiga account na blooger

Abu na farko da za’a fara yi anan shine ziyartar shafin gmail wato www.gmail.com tare da sanya email addreshi da kuma number sirrin bayan an kammala haka sai a ziyarci addreshin blogger wato www.blogger.com ko kuma www.blogspot.com duk wanda aka sanya daga cikin biyun nan zai kai mutum izuwa waje guda ne da zarar na’urar ya karanci wayarka ya tabbar cewa an shiga gmail account to zai kaika izuwa shafi admin dashboard inda ake gudanar da ayyukan shafi.



Hanya ta biyu 

Idan kuma ana so a shiga ta hanya mai sauki za’a iya ziyartar shafin blogger wato www.blogger.com ko kuma www.blogspot.com duk wanda mutum ya sanya daga cikin biyun nan zai kaisa izuwa waje guda ne a can sama wajen hannunka na dama za’a ga inda aka sanya “SIGN IN” a rubuce wanda ake nufin shiga sai a latsa kai muddin anyi hakan zai kai mutum izuwa ga shafin gmail inda za’a bukaci email addreshinsa sai a sanya tare da latsa kan “NEXT” daga bisani kuma zai sake tambayar number sirri sai a basa tare da latsa ma bullin “SIGN IN” mudding an sanya abubuwan da ake bukata daidai zai mutum izuwa ga shafin admin dashboard wato inda dai za’a gudanar da ayyukan shafin.

Yadda ake shiga account wato login a blogger


Sannan duk sain da ake son a dawo dashboard na admin inda ake gudanar da ayyukann shafin za’a je izuwa ga addreshin blogger ne wato www.blogger.com ba tare da sake bin matakan dana gabatar ba face an goge wayar, anyi sabon waya ko kuma ana son shiga da wata wayar shine ya zama dole a sake bin matakan.

Abun kula: Misali ina da email addreshi guda biyu [email protected] da kuma [email protected] sai na bude blogger da [email protected] duk sa’in da nake so na shiga shafina na blogger dole sai na shiga da email addreshin dana bude ba wai dan ina da guda biyu ko fiye da hakan na rudi kaina da cewar zan iya shiga da kowannene wannan ba gaskiya bace sam dole sai da shi wancan dana buden kawai zaiyi aiki saidai in kuma ina son na sake bude wani.


Wannan shine halaccecciyar hanya da ake bi wajen shiga account na blogger ku kasance tare da Duniyar Fasaha domin samun ingatacciyar dabaru daga bangare daban daban; naku a koda yaushe Jikan marubuta kuma sharifin zamani ‘Muhammad Abba Gana’.   

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito

Yadda Za’a Duba Ko Katin Kasa (National I.D) Ya Fito

Idan har an yi rajistar samun katin kasa na dan wasu tsawon lokuta sannan ba’a san ranar da za’a karba katin ba, ko kuma an sha zuwa offishinsu tambayar ko ya matsayin wannan kati yake amma kuma haka zalika ba’a ji sabon labari ba, wata kila kuma an gaji da ziyartar offishinsu har an cire tsanmani. hukumar NIMC a yanzu ta samar da shafin duba matsayin katin ta yanar gizo wanda zai bada damar sanin cewa ko katin ya fito ko dai har yanzu da saura. Ga cikakkaiyar hanyoyin da mutum zai bi ya duba matsayin katin sa na kasa a yanar gizo.

1.==> Abu na farko dai shine, mutum zai ziyarci shafin NIMC a yanar gizo a wannan addreshin: https://touch.nimc.gov.ng/

2.==> Idan an shiga sai a danna mabullin ‘proceed button’ wadda ma’anar sa karasa zuwa gaba



3.==> Daga nan sai mutum ya cika wurin ababen da ake bukata na sunayen sa, wanda akwai wurin cika suna na farko kafin sunan karshen wato sunan uba, sai kuma ya saka lambobi na katin kasa da aka ba shi (yana jikin katin da aka bayar).



4.==> Da mutum ya cike wadannan abubuwa da ake bukata sai ya danna mabullin ‘check now button’. Bayan an danna sai a jira na dan wasu daki kai, yana gama dubawa za’a nuna ma mutum matsayin katin sa. Ya fito ko kuma dai yana hanyar fitowa.


Allah yasa ayi sa’a

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *