Assalamu Alaikum matan gidan nan tare da
fatan kuna cikin koshin lafiya. Na dan tafi hutu ne amma da yardarr Allah na
dawo lafiya. A yau na kawo muku yadda za a kula da gashin kai a lokacin
hunturu. Gashin kawunanmu na bukatar kulawa sosai saboda gashin ‘ya mace na
cikin abin da yake kara mata kyau. Akwai abubuwa da dama wadda ya kamata ki yi
amfani da su kamaru; man zaitun, zuma,
man ‘castor’, ruwan lemun tsami, man kwakwa. Wadannan nau’ukan mai na da
inganci sosai musamman ma wajen kare gashi daga tsinkewa da kuma sa shi karfi,
santsi da sheki.
Man
kasto: Man kastor (castor
oil) na taimakawa wajen gyaran gashin kai a hunturu. A debo man kastor kamar
cokali uku. Sai ki shafa a fatar kai sanan sai a taje a hankali. A tirara tawul
har sai ya yi zafi. Sannan a daura tawul din mai zafi a kai na tsawon minti
goma sha biyar. Bayan haka, sai ayi wanka. Yana hana gashi tsinkewa da hunturu.
Man
zaitun da zuma: A hada
cokali uku na man zaitun da cokali daya na zuma. A kwaba hadin har sai ya
gaurayu sosai, sannan a shafa hadin a kan fatar kai. Bayan mintuna kadan, sai a
wanke da ruwa da sabulun wanke gashi. Kwai, ‘binegar’ da man kwakwa A kada kwai
daya, sai a sa man kwakwa cokali biyu da binegar. A hadin nan hadin waje daya.
Sai a kwaba su. A sa hadin a fatar kai sannan sai a taje gashin kai. A bar
hadin ya jima tsawon minti goma sha biyar. Sai a wanke da ruwan dumi.
Lemun
tsami da man kwakwa: A hada
cokali biyu na man kwakwa, cokali daya na ruwan lemun tsami. Sai a gauraya
hadin har sai ya gaurayu sosai. Sannan a shafa a kan fatar kai. Wannan hadin na
warkar da amosarin kai, da kuma hana gashi tsinkewa.
Man
zaitun: Man zaitun na da
matukar inganci musamman ma ga gashi mai gautsi. Fatar kai na saurin bushewa
saboda hunturu. Idan ana da irin wannan kai, sai a dumama man zaitun a tukunya
idan ya yi zafi, sai a shafa a fatar kai. A ci gaba da murza man a fatar kai
har sai man ya shiga fatar sosai. Sanan sai barshi kamar tsawon minti goma sha
biyar. Bayan haka sai a wanke.
No comments:
Post a Comment