Wani likita a fannin cututtukan mata a
Nijeriya dakta Adewole Akintoyose ya yi kira ga mata da su jimirci cin
kayayyakin itatuwa da na lambu domin kare kansu daga wata cuta mai hana haihuwa
mai suna “endometriosis” a turance.
Adewole, wanda ma’aikaci ne a asibitin St Leo
da ke unguwar Lekki a jahar Lagos ya ce wannan cuta ta fi yawaita a tsakanin
mata ‘yan shekaru 25 zuwa 40.
A fadarsa, Cutar na yin lahani ne ga mahaifa
da kuma kwayayen da ke jikin mace. Likitan ya ce alamomin cuta sun hada yawan
ciwon mara, zafi a yayin saduwa, yawan gajiya, zafi yayin fitsari, da sauran
su.
Sauran alamomin sun hada da rashin haihuwa da
wuri, fara gani jinin haila da wuri, da daina haihuwa a lokacin da ya kamata.
Ya gargadi mata da su rage cin naman shanu,
wanda ya ce ka iya haifar da cutar, ya kuma shawarci su da su kara yawan kayan
itatuwa da na lambun da suke ci, wanda hakan na matukar taimakawa wajen rage
yiwuwar kamuwa da cutar.
No comments:
Post a Comment