Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Abubuwan Da Za A Yi Amfani Da Su Wajen Goge Dauda Da Maikon Fuska

Abubuwan Da Za A Yi Amfani Da Su Wajen Goge Dauda Da Maikon Fuska

Mata da dama ba su san cewa ba ruwa kawai ake amfani da shi wajen wanke dauda da maikon fuska ba.

Fuska tana daya daga cikin ababen da ake fara gani a jikin mutum kafin komai.

Don haka, dole ne a bai wa fuska muhimmanci wajen gyara ta.

Kwanciya da kwalliya na haifar da kurajen fuska sosai musamman idan kayan kwalliyar da aka yi amfani da su ba masu tsada ba ne.

Yana da kyau a rika sanin irin kayan kwalliyar da za a rika shafawa a fuska.

A yau na kawo muku yadda ake goge dauda da maikon fuska.

Yana da kyau mata su rage fita cikin rana a lokacin da rana take da tsananin zafi don hakan na sanya fuska ta hadu da kunar rana.

Ita kuma kunar rana sai an dage kafin ta rabu da mutum, domin canja launin fata take yi sosai ga kuma sanya dauda da maikon fuska.

A samu man zaitun mai kyau ba wanda aka surka shi da wani abu ba. A samu ruwa da murta ko kwalba wanda za a zuba hadin a ciki.

Sannan a zuba zaitun cikin cokali daya (daidai yadda ake so) da ruwan a cikin kwalba. Za a iya cika kwalbar da man zaitun din da ruwa.

Sai a rufe kwalbar da marufinta a girgiza sosai domin hadin ya hadu.

Yana da kyau a gwada hadin man a kan fatar hannu. Domin wadda fatarta ba ta dace da wannan ba, za a ga kuraje suna fesowa.

Sai a zana gazal a fatar hannu a hada hadin sai a goge da shi. Idan bayan minti 30 ba a ga wata illa ba, to za a iya amfani da shi a fuska. Bayan an gama, sai a rufe kwalbar.

A duk lokacin da za a yi amfani da hadin, ya kamata a girgiza kwalbar domin hadin ya gwaurayu.

Sannan a samu auduga a rika tsomawa a hadin ana goge fuskar da shi, yin haka na hana fesowar kuraje a fuska.

Za a iya amfani da ruwan wanke fuska (facial wash) a kullum kafin a kwanta, sannan a goge fuskar da wannan hadin.

Hanyoyin da a za bi domin rage gumin fuska

An camfa cewa, mai yawan gumi a fuska musamman a hanci da cewa wai yana da masifa.

  • Gumin fuska dai a likitance ana kiransa da ‘hyperhidrosis’ shi ne yake sanya yawan gumin fuska; kamar su kan hanci da goshi da saman lebe da wuya da sauransu.

Wani za ki gan shi yana da yawan gumi ba tare da ya yi wani aiki ba.

Akwai abubuwa da dama wadanda suke sanya gumin fuska kamar masu ciwon siga, yawan kiba da hawan jini da bacin rai da sauransu.

Mata wadanda da suke yawan son kwalliya za su tsane gumin fuska domin kuwa, yana bata masu kwalliyarsu.

Babu maganin gumin fuska, amma akwai hanyoyi mafiya sauki wadanda za ki bi domin samin sauki.

Hanyoyi da za ki bi don rage gumin fuska

  •  Ki rage cin abinci wanda ya kunshi borkono ko kayan yaji
  •  Yawan shan bakin shayi yana janyo gumin fuska, amma za ki iya shan ruwa mai yawa don ya taimaka wajen wanke duk maikon jikinki.
  •  Ki rage yin amfani da man shafawa mai maiko domin irin wadannan nau’o’in mai, za su dada maki gumin fuska.
  • Ki nemi mai mara maiko ga fuskar ki.

  • Cin ’ya’yan itatuwa da ganye kamar su; latas da alayyahu da sauransu za su rage gumin fuska.

  • Ki samo ruwan ’vinegar’ sai ki hada shi da zuma mai kyau wanda ba a hada ta da sukari ba, sai ki sha sau uku a rana kafin ki ci abinci.

  • Za ki iya samun ganyen ‘mistletoe’ ki tafasa shi da ruwa kamar na tsawon mintuna 15 sai ki sha yana rage gumin fuska.

  • Robar alkama, tana da kyau gurin rage gumin fuska. Ki tafasa ta, sai ki sha ruwan domin robar alkama, tana kunshe da sinadarin Bitamin C da kuma Bitamin B-12 wajen rage maiko da kuma gumin fuska.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *