Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Hanyoyin Da Kafofin Sada Zumunta Ke Samun Kudaden Shiga

Hanyoyin Da Kafofin Sada Zumunta Ke Samun Kudaden Shiga

Tsawon lokaci masu karatu ba su gushe ba wajen tambayata kan wacce hanya ce ko kafofin sada zumunta na zamani suke samun kudaden shigarsu?

Galibin lokuta idan aka yi mini wannan tambaya nakan ba da amsa a takaice ne, musamman idan ta hanyar sakon tes ne ko ta shafin Facebook.

A yau in Allah Ya so zan yi bayani a fayyace, dalla-dalla, sanka-sanka kan wadannan hanyoyi.

Amma kafin nan, zan so mu fahimci tsarin samar da bayanai a shafukan Intanet, tsakanin jiya da yau.

 

Wannan zai taimaka mana wajen fahimtar sauran bayanan da za su biyo baya, cikin sauqi.

 

Tsarin samar da bayanai a Intanet: Jiya da yau

 

Akwai tsari biyu na samar da bayanai a giza-gizan sadarwa na Intanet.

 

Wadannan hanyoyin samar da bayanai dai, daya ne asali daga cikinsu, a yayin da daya hanyar ta samo asali ne daga hanyar farko.

 

Ga bayanin kowane daga cikinsu nan.

 

Bayanan Mai Shafi: (Ownergenerated Content)

 

Hanyar farko ta samo asali ne daga farkon lokacin da aka samar da fasahar Intanet zuwa shekarun 1990, galibin bayanan da ke shafukan Intanet duk wadanda masu shafukan ne suka samar.

 

A wannan zamani, duk shafi ko gidan yanar sadarwa za ka ci karo da shi a Intanet a dauke yake da bayanan da asalin maginin shafin ko gidan yanar ya zuba.

 

Idan shafin jarida ne, za ka tarar da labarun da suke shafukan gida na yanar sadarwar duk na mai shafin ne, wadanda ya rubuta don labarta abin da ya gani.

 

Idan shafin sayar da kayayyaki ne, za ka tarar da bayanan hajojin da kuma hotunansu, duk na mai shafin ne.

 

Galibin bayanan da suke Intanet a wannan lokaci har wa yau, duk zallar rubutu ne, sai ’yan hotunan da ba za a rasa ba.

 

Zuwa qarshen shekarun 1990 ne aka samu ci gaban fasahar gina shafukan Intanet ta amfani da yaren JavaScript da Flash na Kamfanin Macromedia.

 

Wannan yanayi ya samar da bayanai masu motsi na bidiyo ko flash da sautuka da ake iya tu’ammali da su a shafukan yanar sadarwa.

 

Har zuwa karshen shekarun 1990, babu shafun sada zumunta irin wadanda ake da su a yau.

 

Shafukan da suka shahara a wancan lokaci su ne “Zaurukan Intanet” ko “Kauyukan Intanet” na Kamfanin Yahoo! da MSN – irin su “Yahoo Groups” da “MSN Groups”, sai kuma “Google Groups” da aka samar a karshe.

 

Dandalin sada zumunta da ya shahara, wanda yake kama da irin abin da muke da su a yanzu, shi ne shafi ko dandalin “MySpace” wanda a yanzu ya dade da macewa.

 

A wannan marhala na wanzuwar Intanet a duniya, bayanan da suke shafukan Intanet ko gidajen yanar sadarwa, duk na asalin mai shafin ne, ba na ma su ziyara ba.

 

Galibin masu ziyara sai dai su yi tsokaci kan abin da mai shafin ya rubutu ko ya wallafa a shafinsa.

 

Wannan tsari da nau’in bayanai shi ake kira: “Owner-generated Content.”

 

Bayanan Masu Ziyara: (Usergenerated Content)

 

Daga shekarar 2000 zuwa yau kuma, tsari da kintsin shafuka da fasahar Intanet sun canja matuka.

 

An samu ci gaba wajen hikima da fasaha da tsarin aikawa da karbar bayanai a giza-gizan sadarwa na Intanet, fiye da kowane lokaci a tarihin wannan fasaha.

 

Sai salon masu samar da masu bayanai ya canja daga ilimantarwa kadai zuwa kasuwanci da neman kudi.

 

Kuma tunda wannan fasaha ta Intanet an gina ta ce a turbar ilimi wadda ingancinta ta rataya ga ingancin bayanai, wannan ya sa samuwa da bunqasar wannan salo ya habaka sosai.

 

A karkashin wannan tsari, galibin bayanan da suke shafukan Intanet na masu ziyara ne, wadanda mai shafin ke ba su damar samar da shafi na kansu, ya tanada musu abubuwan da za su yi amfani da su wajen samar da bayanai.

 

A kan haka ne dandalin sada zumunta na wannan zamani suke gudanuwa.

 

Idan ka yi rajista a shafin Facebook misali, da zarar ka hau shafinka, za ka tarar da komai kake bukata wajen samar da bayananka a nau’in zallan rubutu (Tedts) ko hotuna (Images) ko bidiyo (Video) ko sauti (Audio).

 

Bayan haka, idan kana bukatar gina manhaja ta musamman da kake son wadansu su yi amfani da ita, duk za ka iya haka cikin sauki, muddin ka mallaki qwarewa a kan haka.

 

Wannan tsari na bai wa mai ziyara damar samar da bayanai da kansa, shi ake kira: “User Content Style,” su kuma bayanan da aka samar da su ta wannan hanya ana kiransu: “User-generated content.”

 

Kuma dukkan shafuka da dandalin sada zumunta na zamani-na kwamfuta da na wayar salula- an gina su ne a karkashin wannan tsari.

 

Manufar yin haka shi ne, tunda ra’ayoyin jama’a ne da kansu, wadanda suke bayyana hakikanin manufofinsu, to, amfani da wadannan bayanai da suka samar da kansu zai taimaka wajen samar da hajojin kasuwanci.

 

Domin ta wadannan bayanai ne ake sanin qasashensu da manufofinsu na siyasa, da dandanonsu a rayuwa, da jinsinsu, da addininsu da abin da suke so da wanda ba sa so.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *